APC Ba Ta Cika Alkawuranta Ba – In Ji Wani Babba A APC

Tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya nemi afuwar ‘yan Najeriya kan gazawar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) wajen cika alkawurran da ta dauka tun bayan karbar mulki.

Fayemi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a tashar Channels Television da yammacin jiya Alhamis.

“Dole ne mu nemi afuwar ‘yan Najeriya. Ba mu sami damar cika duk alkawurran da muka dauka ba,” in ji shi.

Ya bayyana cewa rashin aiwatar da alkawurran ba saboda rashin iya mulki bane, “amma akwai wasu matsaloli na tsarin gwamnati da suka hana mu cimma burinmu.”

“Gaskiya ba mu yi isasshen kokari ba wajen kyautata rayuwar ‘yan Najeriya. Saboda haka, ba zan yi kasa a guiwa ba wajen neman afuwarsu,” in ji shi.

Tun a shekarar 2015 APC ta karbi mulki daga hannun PDP da alkawarin yaki da cin hanci da rashawa, inganta tattalin arziki da kawo karshen rashin tsaro.

Comments (0)
Add Comment