Jam’iyyar APC reshen Jihar Jigawa ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Gwamna Umar Namadi tare da amincewa cewa ba za ta yarda wani ya tsaya takara da shi ba a zaɓen shekarar 2027, lamarin da ya sa ya zama ɗan takararta tilo a matakin gwamna.
Wannan matsaya ta fito ne yayin ci gaba da gudanar da shirin “Gwamnati da Jama’a” da Gwamna Namadi ke yi a dukkan ƙananan hukumomin jihar, inda a wannan makon aka gudanar da taron a ƙaramar hukumar Guri.
Tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai kuma jigo a jam’iyyar APC ta ƙasa, Hon. Faruk Adamu Aliyu ne ya miƙa wannan bukata ga ƴan jam’iyyar, yana mai cewa, “Ya kamata mu tsaya tsayin daka wajen goyon bayan Gwamna Namadi domin tabbatar da nasarar APC a 2027.”
WANI LABARIN: Gwamna Namadi Ya Ce APC Za Ta Ci Gaba Da Inganta Rayuwar Jama’ar Najeriya
Daga nan ne dukkan wakilan majalisa da suka halarci taron – ciki har da Sanata Ahmad Abdulhamid Malam Madori, ɗan majalisar wakilai Hon. Abubakar Hassan Fulata, da Kakakin Majalisar Jihar Jigawa Hon. Haruna Aliyu Dangyatum – suka miƙa ƙudirin neman amincewa da takarar gwamnan a taron.
Wannan mataki ya biyo bayan gamsuwar da jiga-jigan jam’iyyar suka nuna bisa yadda Gwamna Namadi ke tafiyar da mulki da kuma ƙoƙarin tabbatar da cigaban jihar.
A cewar wakilan, amincewa da takarar gwamnan ba tare da hamayya ba zai ba jam’iyyar damar hada kai da mai da hankali wajen ci gaba da shimfiɗa tsare-tsare masu amfani ga al’umma.
Wannan matakin ya zo ne a daidai lokacin da wasu zaɓaɓɓun shugabanni a matakai daban-daban ke bayyana sha’awar sake tsayawa takara, lamarin da ke ƙara tabbatar da fara girgiza fagen siyasar zaɓen 2027.