AREWA A CIKIN DUHU: Mahimman Bayanai 10 Kan Matsalar Rashin Wutar Lantarki Da Ke Ƙara Ta’azzara

  1. Tsananin Rashin Wutar Lantarki: Jihohi sha bakwai na Arewacin Najeriya na fuskantar rashin wutar lantarki na fiye da makonni biyu, inda jihohin Kaduna, Kano, Jigawa, da Gombe suka fi shan wahala. Iya jihohin Neja da Kwara ne kawai suke da wuta.
  2. Tasiri Kan Tattalin Arziki: Rashin wutar lantarkin ya kassara harkokin kasuwanci a yankin, yana kuma cigaba da jefa kasuwanni da yanayin tattalin arziki cikin matsananciyar matsala.
  3. Dalilin Rashin Wutar: Hukumomi sun alaƙanta rashin wutar da gangancin lalata turakan lantarki, musamman layin wutar Shiroro zuwa Kaduna, wanda ke da matuƙar mahimmanci wajen isar da wuta ga Arewacin Najeriya.
  4. Kiran Gwamnoni Don Ɗaukar Mataki: Gwamnonin Arewa, ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Yahaya, sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta taimaka cikin gaggawa wajen ƙara yawan layin wutar da kuma bunƙasa hanyoyin samun wuta ta wasu hanyoyin na daban don samar da ingantacciyar wutar lantarkin a yankin.
  5. Martanin Shugaban Ƙasa: Shugaba Bola Tinubu ya umurci Ministan Wutar Lantarki da ya hanzarta gyara matsalar lantarkin, tare da ba da izini ga sojoji su tsare injiniyoyin da ke aikin gyaran da kuma kare su daga masu yunƙurin lalata kayan wutar.
  6. Ƙalubalen Tsaro: An samu jinkiri wajen gyaran wutar ne saboda matsalar tsaro ga ma’aikata. Don haka aka haɗa hannu tare da mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa da kuma sojoji domin tabbatar da tsaron ma’aikatan da ke gyaran layin wutar.
  7. Kiran Bunƙasa Wutar Lantarki Ta Hanyoyin Na Daban: Manyan shugabanni ciki har da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, sun jaddada buƙatar zuba jari a hanyoyin samun wuta ta wasu hanyoyin, musamman ta hanyar amfani da ruwa kamar aikin da aka yi a Dam ɗin Challawa a Kano.
  8. Matsalar Tsofaffin Kayayyakin Wutar Lantarki: Rashin ingancin kayayyakin lantarki na Najeriya wanda ya shafe shekaru, yana ƙara tsananta matsalar. Gwamnati ta bayyana matuƙar buƙatar inganta tsarin, tare da tabbatar da samun tsaron kayayyakin lantarkin.
  9. Zuba Jari A Harkar Solar: Gwamnatin tarayya ta sanar da ƙudurin masu saka jari don zuba tsakanin dala biliyan $1 zuwa $2 a cikin harkar solar, da nufin samar da megawatt 50 a kowace jiha cikin jihohi goma sha tara na Arewa, don rage nauyin da ke kan layin wutar lantarki na ƙasa.
  10. Martanin Jama’a Da Na Ƴan Siyasa: Rashin wutar lantarkin ya haifar da cece-kuce a ɓangaren ƴan siyasa, inda ƴan adawa ke tambayar ingancin manufofin gwamnati. A yayin da jam’iyyar APC mai mulki ke cewa akwai ci gaba a sha’anin wutar lantarkin, ƙalubalen tsaro da inganta kayan aiki na gaban gwamnati don shawo kansu.
Arewa
Comments (0)
Add Comment