AREWA: Wata Ƙungiyar Kare Yankin Ta Ce An Ware Arewa A Samar Da Ci Gaba, Ta Shirya Tunkarar Zaɓen 2027

Kungiyar Arewa Defence League (ADL) ta yi kira kan abin da ta kira wariya ga Arewa a harkokin ƙasa, tana shirin magance matsalar kafin zaɓen 2027, kamar yanda wakilin PUNCH ya rawaito.

A wani taro a Arewa House, Kaduna, ƙungiyar ta bayyana cewa Arewa ta yi fice a muhimman muƙamai, amma an yi watsi da ita a tattalin arziƙi, an bar ta da giɓi a ababen more rayuwa, kuma tsaro ya taɓarɓare a ƙarƙashin jerin gwamnatocin tarayya da aka yi.

Shugaban ADL, Murtala Abubakar, ya ce, “mun lura da tsanani na wariyar siyasa, tattalin arziƙi da gine-gine, (ba zamu bari) wannan ya ci gaba ba,” yana mai cewa Arewa ba za ta ƙara yin shiru ba.

Takardar bayan taron ta ce akwai “banbance-banbancen arziƙi masu tayar da hankali” tsakanin Arewa da sauran yankuna, inda rabon kasafin kuɗi da wuraren ajiye manyan ayyuka ke fifita wasu sassa duk da wadatar noma da ma’adinan da Arewa ke da su.

Game da tsaro, ta ce, “wahalar jama’armu ta zama mai tsanani; ƴan bindiga da ta’addanci sun durƙusar da kasuwanni, gonaki, makarantu da rayuwarmu, ɗaukar mataki daga tarayya ya yi rauni kuma bai da tabbas.”

Ƙungiyar ta kuma zargi gwamnatoci da karya ƙa’idar raba-daidai ta ‘federal character’ don rage tasirin Arewa a tsaro, gwamnati da cibiyoyin tattalin arziƙi, tare da sanar da shirin “Charter of Northern Grievances” da gangamin wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a gabanin 2027. Abubakar ya ƙara da cewa, “ba za a sake ɗaukar ƙuri’unmu da wasa ba,” tare da ƙoƙarin haɗa kai da sauran yankuna domin samar da “Najeriya mai adalci yadda kowane yanki zai samu damar bunƙasa.”

Comments (0)
Add Comment