ASUU Ta Ƙara Yin Barazanar Tsunduma Yajin Aiki, Za A Gudanar Da Zanga-Zanga A Jami’o’i

Ƙungiyar malaman jami’o’i ta ASUU ta yi barazanar tsunduma yajin aiki na ƙasa baki ɗaya domin gwamnatin tarayya ba ta cika alƙawuran da ta ɗauka ba.

A taron manema labarai a Jami’ar Jos, Shugaban ASUU, Christopher Piwuna, ya ce malamai sun shafe shekaru biyu suna jiran aiwatar da yarjejeniyoyi amma har yanzu shiru.

Ya lissafo matsaloli kamar sabunta yarjejeniyar 2009, bashin albashi, dakatar da ƙarin girma da kuma halin tsarin ritayar malamai.

Piwuna ya ce “Gwamnatin Tarayya ta rufe kunnenta ga koke-kokenmu duk da mun rubuta wasiƙu da dama.”

Ya kuma bayyana cewa “mambobinmu ba sa buƙatar rance; muna buƙatar aiwatar da yarjejeniyar da za ta ƙara darajar albashinmu ne.”

Ƙungiyar ta ce za ta jira sakamakon taron gwamnati na ranar 28 ga Agusta amma za ta gudanar da zanga-zangar nuna damuwa a faɗin jami’o’i.

Piwuna ya yi gargaɗin cewa “lokaci na ƙurewa ne; ba za mu iya ci gaba da jira har a lalata makomar jami’o’in Najeriya ba.”

Comments (0)
Add Comment