ASUU Ta Yi Allah-wadai Da Sake Sunan Jami’ar Maiduguri, Ta Ce Za Ta Damfara Gwamnati A Kotu

Ƙungiyar malaman jami’a, ASUU reshen Jami’ar Maiduguri ta ce ta “ta matuƙar ƙin yarda kuma ta yi fatali” da matakin gwamnatin tarayya na sauya sunan jami’ar zuwa Muhammadu Buhari University, Maiduguri.

A wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Abubakar Mshelia, da mataimakinsa Peter Teri suka sanyawa hannu bayan taron gaggawa na majalisar ƙungiyar da aka gudanar a ranar 24 ga Yuli, ƙungiyar ta ce za ta ɗauki matakin shari’a domin hana aiwatar da matakin.

ASUU ta bayyana cewa taron ya samu halartar mambobin ƙungiyar, wakilan ɗalibai, da sauran manyan masu ruwa da tsaki a harkar jami’ar.

“Bayan tattaunawa mai zurfi, majalisar ASUU ta cimma matsaya ɗaya ta ƙin amincewa da sauya sunan jami’ar, tare da buƙatar a janye matakin nan take ba tare da wani ɓata lokaci ba,” in ji sanarwar.

WANI LABARIN: Majalisar Wakilai Zata Kama Gwamnan Babban Bankin Najeriya Bisa Saɓa Dokokin Kula Da Kuɗaɗe

Ƙungiyar ta bayyana sauya sunan a matsayin “watsi da ikon ƴancin kai na jami’o’i, da tozarta al’adun ilimi, da kuma keta mutuncin tarihi da martabar jami’ar da ke da shekaru fiye da hamsin.”

Har ila yau, ASUU ta ce “ba a tattauna da jami’ar ba, ko da tsofaffin ɗalibai ko sauran masu ruwa da tsaki kafin ɗaukar wannan hukuncin da ba shi da tushe.”

A ƙarshe, kungiyar ta ce za ta yi amfani da duk hanyoyin shari’a da suka dace domin tabbatar da cewa martabar Jami’ar Maiduguri ta kasance yadda take, tare da neman haɗin gwiwa daga ofishin ASUU na ƙasa da majalisar dokoki domin hana wannan sauyi.

Comments (0)
Add Comment