Atiku, Gwamnoni Da Manyan PDP Sun Tattauna Kan Makomar Jam’iyyar

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, a zaɓen da ya gabat, Atiku Abubakar da wasu daga cikin gwamnonin da aka zaɓa ta jam’iyyar sun fara tuntuɓa kan makomar jam’iyyar.

Abubuwan da aka tattauna a zaman na sirri da aka gudanar a gidan tsohon Ministan Ƙasashen Waje a mulkin Sani Abach, Chief Tom Ikimi da ke Maitama a Abuja sun ci gaba da kasancewa sirri.

Wata majiya da take masaniya kan taron tattaunawar ta bayyanawa jaridar VANGUARD cewa, tattaunawar na daga cikin ƙoƙarin tuntuɓa a tsakanin shugabannin jam’iyyar.

Labari Mai Alaƙa: El-Rufa’i Zai Haɗa Faɗa Tsakanin Tinubu Da Shettima – Shehu Sani

Majiyar ta ƙara da cewa, wannan wani fari ne tattaunawa da dama da zata gudana domin ƙara ƙarfafa jam’iyyar, sannan kuma shiri ne na tunkarar babban taron da za a yi a mako mai zuwa.

Gwamnonin da suka halarci zaman sun haɗa da: Gwamna Bala Mohammed, Jihar Bauchi; Gwamna Sheriff Oborevwori, Jihar Delta; Gwamna Godwin Obaseki, Jihar Edo; Gwamna Ademola Adeleke, Jihar Osun; Gwamna Caleb Mutfwang, Jihar Plateau; da Gwamna Dauda Lawan, Jihar Zamfara.

Atiku AbubakarPDP
Comments (0)
Add Comment