Ba A Samu Sanya Hannun Jari Ko Na Sisi Ba A Wasu Jihohi 8 Na Najeriya

Akalla jihohi takwas ne ba su iya jan hankalin masu sanya hannun jari daga kasashen waje ba amma bashin da suka ciyo ya kai naira biliyan 194.09 a tsakanin shekarar 2019 da 2022 kamar yanda jaridar PUNCH ta gano.

Bayanai daga Hukumar Kididdiga ta Kasa sun nuna cewa, jihohin Bayelsa, Gombe, Ebonyi, Jigawa, Kebbi, Taraba, Yobe da Zamfara ne ba su iya jan hankalin masu saka hannun jarin ba daga kasashen waje.

Haka kuma bayanai daga Ofishin kula da Basussuka na Kasa, DMO, sun nuna cewa, a daidai shekarar 2019, basussukan da ake bin wadannan jihohi yana naira biliyan 710.38.

To amma a shekarar 2022, jimillar bashin da ake bin jihohin ya kai naira biliyan 904.47, abin da yake nuna karuwar naira biliyan 194.09 cikin shekaru uku kacal.

Wadannan basussuka sun hada da na cikin gida da kuma wadanda aka ciyo daga ketare kamar yanda DMO ya bayyana.

A shekarar 2019, lokacin da jihohi takwas din ke da bashin cikin gida na naira biliyan 564.69, bashinsu daga ketare yana naira biliyan 145.69.

A shekarar 2022, basussukan wadannan jihohi na cikin gida ya kai naira biliyan 758.39 yayinda shi kuma bashin da suka ciyo daga ketare ya karu kadan inda ya koma naira biliyan 146.08.

Wannan ya nuna cewa, jihohin sun ciyo mafi yawan basussukan ne daga masu bayar da bashi na cikin gida.

Bayanan sun kuma nuna cewa, jihohin da suka fi ciyo bashin a shekarar 2019 sune Bayelsa (N147.93bn), Gombe (N84.01bn), da Taraba (N82.32bn).

A shekarar 2022 kuma Bayelsa ta ci gaba da kasancewa a kan gaba da yawan bashin naira biliyan 146.37, sai Gombe ta kara zuwa ta biyu inda take da bashin naira biliyan 139.32, sai kuma Zamfara da ta doke Taraba ta zo ta uku da yawan bashin da ya kai naira biliyan 122.2, yayinda Taraban ke da bashin naira biliyan 87.96.

A bangaren bashin da aka ciyo daga ketare kuma, jihohin Ebonyi mai bashin dala miliyan 65.2; Bayelsa mai bashin dala miliyan 59.55 da Kebbi mai bashin dala miliyan 44.03 ne suka zama a kan gaba a shekarar 2019.

A Shekarar 2022 kuma, Bayelsa ce ta zo na farko yawan bashin ketare inda ta kere Ebonyi da yawan bashin dala miliyan 60.39; Sai Ebonyin mai yawan bashin dala miliyan 58.57; Sai kuma Taraba wadda ta kere Taraba a wannan karon da yawan bashin da ya kai dala miliyan 46.47; Sai kuma Kebbin mai yawan bashin da ya kai dala miliyan 40.93.

A rahotonta na watan Disambar 2022, Nigeria Development Update ta ce, Bankin Duniya ya bayyana cewa, basussukan da ake bin jihohi zai haura kaso 200 cikin 100 na kudaden da aka samu a shekarun 2022 da 2023.

Rahoton ya bayyana cewa, “Girman bashi ga matsakaitan jihohi zai karu daga kaso 154.6 cikin 100 na kudaden shiga a shekarar 2021 zuwa sama da kaso 200 cikin 100 a shekarun 2022 da 2023.”

Bankin Duniyar ya kar da cewa, karuwar basussukan zai faru ne saboda karancin kudaden da jihohi suke samu daga Asusun Tarayya, abin da zai kara raunana harkokin kudaden jihohi.

Ya kuma ce, sanya hannun jarin ‘yan kasashen waje a Najeriya zai ci gaba da kasancewa mai rauni saboda karancin kudaden canji, matsalolin tsaro da sauran matsalolin tsare-tsare.

Da yake magana a kan lamarin, Farfesa a bangaren tattalin arziki, Jami’ar Uyo, Farfesa Akpan Ekpo ya shaidawa PUNCH cewa, rashin masu sanya hannun jarin a jihohi da kuma matsalar tsaro ne manyan dalilan da suka jawo rashin sanya hannun jarin a jihohi.

Da yake bayyana nasa hangen, masanin tattalin arziki, Aliyu Ilias ya ce, jihohin har yanzu ba su iya gina kansu a matsayin masu son bunkasar masana’antu da samar da kasuwa ba ta yanda zasu ja hankalin masu sanya hannun jari.

Aliyu Ilyas ya kuma yi kira ga jihohi da su samu wani bangare mai karfi da su bunkasa a matsayin hanyar da zasu ja hankalin masu sanya hannun jari daga kasashen waje.

Hannun JariJihohi
Comments (0)
Add Comment