Ba Da Sani Na Na Ciri Kuɗi Har Sau 5 A Katin Kostoma Ba – Wani Ma’aikacin Banki

Wani tsohon ma’aikacin banki mai suna, Uchenna Emmanuel ya amsa laifin cewar ya yi amfani da katin kostoma wajen cirar kuɗi har sau biyar.

Wanda ake zargin, wanda tsohon mai biyan kuɗi a banki ne, ya amsa laifin nasa ne jiya Juma’a bayan ƴansanda sun yi ram da shi a Akure, babban birnin Jihar Ondo.

A bayaninsa, wanda ake zargin ya ce, ya ciri kuɗi daga asusun kostoma har sau biyar domin ya sayi wani abu na naira 35,000.

Labari Mai Alaƙa: Za A Ci Gaba Da Tsare Waɗanda Ake Zargi Da Ƙaryar KAROTA Su 25 A Kano

Ya ce injin POS ɗin da yai amfani da shi yana da matsala ne, abin da ya sa ya samu damar yin amfani da lambarsa ta ƙashin kansa wajen yin damfarar.

Ya kuma ce, bayan manajan bankin da yake aiki ya gano abin da ya aikata ya kore shi daga aiki nan take.

Ya ƙara da cewa, sun yi musun ta ya akai ya samu lambar PIN ta kostoman, inda ya tabbatar musu da cewa da PIN ɗinsa yai amfani ba da na kostoman ba, abin da ya sa ɗaya daga cikin ƴansandan fitowa da katin ATM ɗinsa don a gwada, aka gwada kuma wanda ake zargin ya saka PIN ɗinsa kuma kuɗi ya fita.

ATMDamfaraPIN
Comments (0)
Add Comment