Ba Neman Kuɗi Na Zo Ba, Aiki Ne Ya Kawo Ni, In Ji Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya tabbatarwa ƴan Najeriya cewa gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen kawo canje-canje na gari, tare da samar da cigaban ƙasa ta fannin gine-gine, tsaro da abinci, ilimi da kuma dauwamammen tattalin arziki.

A wata ganawa da Ƙungiyar Tsofin Shugabanin Majalisar Tarayya, ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban majalisar dattawa Ken Nnamani, Shugaban ya jaddada cewa bai zo neman kuɗi ko cin gajiyar muƙami ba, sai dai domin yiwa kasa hidima.

Ya ce, “Ba neman kuɗi na zo yi ba, na zo ne domin yin aiki. Na nemi kuri’un ƴan Najeriya, su kuma suka bani.”

A cewar Bayo Onanuga, wanda ke magana da yawun Shugaban, taron ya samu halartar tsofaffin shugabanni 16 na majalisun da suka haɗa da tsofin shugabannin majalisar dattawa, majalisar wakilai, da mataimakansu.

Shugaba Tinubu ya godewa tsofin shugabannin bisa goyon bayansu, kuma ya buƙace su da su cigaba da haɗa kai domin cigaban ƙasa.

Ya bayyana cewa, duk da ƙalubalen da aka fuskanta a baya, ya kamata a haɗa hannu wajen ganin Najeriya ta samu cigaban da take buƙata.

Haka zalika, Shugaban ƙasar ya yi alƙawarin ci gaba da inganta rayuwar al’umma ta hanyar gyara gine-ginen makarantu, samar da tsaro da haɓaka tattalin arziki.

Bola Ahmed Tinubu
Comments (0)
Add Comment