Ba Za Mu Ƙyale A Lalata Muhimman Kadarorin Ƙasa A Jihar Rivers Ba – Sojoji

Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa ba za ta zuba ido ta bar wasu mutane su lalata muhimman kadarorin ƙasa ba, musamman a Jihar Ribas, inda aka samu fashewar bututun mai a kwanan nan.

Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Tsaro, Manjo-Janar Markus Kangye, ne ya bayyana haka yayin da yake gabatar da rahoto kan ayyukan sojoji a faɗin ƙasar, a yau Alhamis a Abuja. 

A cewarsa, rundunar soji na ƙoƙarin kare kadarorin man fetur na ƙasa a yankin Neja Delta, kuma ba za su bari ƴan ta’adda su ci gaba da ɓarnata su ba. 

Ya ce, “Kwana-kwanan nan an samu hare-hare da fashewar bututun mai a Ribas. Ba zai yiwu mu ƙyale wasu ɓata-gari su lalata kadarorin ƙasa ba, domin an tura sojoji ne don su kare su.”

Manjo-Janar Kangye ya kuma bayyana cewa sojojin Operation Delta Safe sun daƙile yunƙurin satar ɗanyen mai da darajarsa ta kai Naira biliyan 461.7 a cikin mako guda a yankin Kudu maso Kudu.

Ya ƙara da cewa an ƙwato lita 247,629 na ɗanyen mai da kuma lita 198,374 na man dizal da aka tace ba bisa ka’ida ba. 

Bayan haka, dakarun soji sun lalata tanda 36 da ake dafa man fetur da su, tare da ramuka 42, kwale-kwale 28, tankokin ajiya 33, ganguna 65, da kuma wuraren tace mai na haramtacciya guda 21. 

An kuma kama mutane 17 da ake zargi da aikata laifin satar mai, inda aka ƙwato bindigogi da alburusai, da babura, da wayoyin hannu da wasu motocin da ake zargi an yi amfani da su wajen aikata laifukan.

Sojoji sun yi gargaɗi ga duk wani mai hannu a ayyukan fashewar bututun mai da satar ɗanyen mai, tare da cewa za su ci gaba da gudanar da ayyukansu don kare kadarorin ƙasa daga barazanar ɓata-gari.

Comments (0)
Add Comment