Ba Zai Yiwu Ka Ƙaƙabawa Mutane Haraji Ba Tare Da Ƙara Musu Kuɗin Da Suke Samu Ba – Ndume

Sanata Ali Ndume ya kushe batun sabon haraji na kula da hadahadar banki ta intanet, inda ya ce, rashin dacewa ne gwamnati ta cigaba da cajar ‘yan ƙasa haraje-haraje ba tare da ta yi wani abu da zai ƙara musu kuɗin shigar da suke samu ba.

Ɗan Majalissar Dattawan mai wakiltar Borno ta Kudu wanda ya baƙunci shirin Politics Today na Channel Television a jiya Juma’a ya ce, wannan sabon haraji na kula da hadahadar banki ta intanet zai ƙara matsin rayuwa ne ga ƴan Najeriya.

Ndume ya ce, “Ba zai yiwu kai ta lodawa mutane haraje-haraje a lokacin da ba ka ƙara musu kuɗin da suke samu ba. Ba ka faɗaɗa musu hanyoyin samunsu ba, ba ka ƙara musu shi ba. Bana cikin waɗanda suke goyon bayan sanya wa mutane haraji.”

A kwanakin baya ne aka yi wa dokar tsaron intanet gyara a Majalissar Tarayya wadda Ndume ke ciki, to amma ya ce, duk da ya goyi bayan sabunta dokar, abun takaici ne da bai gano cewar akwai wannan ɓangaren da zai takurawa ƴan Najeriya a dokar ba.

A ranar 6 ga watan Mayun nan ne, wata sanarwa daga Babban Bankin Najeriya ta umarci dukkan bankuna da sauran kafofi masu hadahadar kuɗaɗe da su na cire kuɗin bayar da kariyar asusun kwastomominsu daga matsalolin intanet wanda ya kai rabin kaso ɗaya cikin ɗari na hada-hadar da aka yi.

Comments (0)
Add Comment