Ba Zan Nemi Takarar Shugaban Ƙasa A 2027 Ba Matuƙar Goodluck Zai Nema, In Ji Bala Mohammed

A lokacin da ake cigaba da hasashe da kiraye-kiraye kan babban zaɓen shekarar 2027, ɗaya daga cikin waɗanda ake sa ran zasu nemi takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed ya ce, ba zai nemi takarar ba, matuƙar tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan ya yanke shawarar sake tsayawa.

Gwamna Bala Mohammed ya bayyana hakan ne a ranar Juma’ar nan lokacin da wata ƙungiya mai suna Save Africa Initiative ta kai masa ziyara tare da nemansa da ya nemi takarar shugaban ƙasa.

Ƙungiyar ta kuma ba shi kyautar girmamawa ta ‘Gwarzon Zaman Lafiya, Haɗinkai da Samar da Cigaba’.

Gwamnan na Jihar Bauchi wanda tsohon Ministan Abuja ne ƙarƙashin gwamnatin Jonathan ya ce, tsohon shugaban ƙasar yana da ƙwarewa sama da shi, kuma zai yi abin da ya dace idan har ya samu dama.

Ya ce ya yarda da tsarin karɓa-karɓa da PDP ke amfani da shi, haka kuma a yanzu juyin mutanen Kudu ne su yi shekara takwas, amma akwai buƙatar su nuna sun cancanci hakan.

Zaben 2027
Comments (0)
Add Comment