Ba Zata Canja Zani Ba, Gwmantin Tinubu Irin Ta Buhari Ce, Ƴan Najeriya Su Shirya Karɓar Ƙaddara

Daga: Ahmed Ilallah

Da dukkan alamu fa, wahala bata ƙare ba, kuma babu ranar wucewarta a nan kusa, Ƴan Nijeriya mu shirya karɓar ƙaddara. Ita dama ƙaddara a kwai wadda Allah ya kan kawo ta domin jarrabar bayinsa, ko kuma sakayyar yin gangancinsu, wajen damar da suka samu na yiwa kansu dai dai ko akasin hakan.

Ita kyakkyawar Juma’a tun daga Laraba a ke gane ta, alamu kan nuna yiwuwar kyawun al’amari a farkonsa, tun kafin a yi nisa. Shi mutum ya sha babban ne da dabba, domin yin amfani da hankalinsa daɗi da ƙari da ilimin da Allah ya hore masa, wajen nazartar abin da ke gabansa don hango abin da ke gaba da shi ko mai zuwa.

Jawabin Shugaba Tinubu da ya yi wa ƴan Najeriya ranar 31 ga watan Yuli da kuma yin nazarin da irin mutanen da ya miƙawa Majalisar Dokoki ta Ƙasa, domin tantancewa, don naɗasu Ministoci kuma mambobin Majalissar Zartarwa ta Kasa, zamu iya nazartar irin takarawar da wannan gwamnatin zata yi.

Daman ƴan Najeriya fa suna cikin tsananin rayuwa tun a mulkin baya na Shugaba Buhari, sai ga shi matakin da ita wannan gwamnatin ta Shugaba Bola Tinubu ta ɗauka na cire tallafin man-fetur, da kuma matakin gwamnatin na ragewa Naira daraja, sun yi bazata wajen ƙara saka mutanen Najeriya cikin tsananin rayuwa fiye da baya, kuma da dukkan alamu, ita ma wannnan gwamnati ta zo, babu kintsattsen shiri na ko-ta-kwana ga ƴan Najeriya a yanayin da suke ciki a yanzu. Wanda da ma a nazari na tattalin arziki, a kwai hasashen tashin kayan buƙatu na yau da kullum da kuma yiwuwar ƙaruwar talauci a wajen ƴan ƙasar.

Bayanin Shugaba Tinubu Da Yanayin Da Ƴan Ƙasa Ke Ciki

Ko shakka babu, in a ka yi nazari a kan bayanan Shugaba Tinubu game da tsare tsarensa, na fasalta tattalin arzikin Najeriya da kuma tsarinsa na kawo wa ƴan Najeriya sauƙin rayuwa, zai kasance kamar karatun labari ne irin wanda  tsohon shugaba Buhari ya sha yi, ba tare da ganin canji ba.

In aka yi duba da irin tanade-tanaden da aka ce za a yi wa ƴan Najeriya, kusan babu irin wanda gwamnatin baya ba ta yi ba, amma babu wata gagarumar nasara, wajen canja rayuwar ƴan Najeriya.

Bayar da bashi ga manyan masana’antu, ita kanta gwamantin Buhari ta bawa masana’antun sarrafa magunguna na  ƙasarnan bashin da ya kai naira biliyan ɗari (N100B) ta hannun Babban Bankin Najeriya (CBN).

Ko da ƙananan ƴan kasuwa da manoma da Shugaba Tinubu ya ce za a tallafawa da bashi don fita daga wannan raɗaɗin, babu wani abu da zai canja. Domin gwamantin Buhari da ta gabata ta bayar da bashin da ya wuce naira biliyan ɗari biyu (N200B) ga kimanin ƙananan ƴan kasuwa miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar (1.5m). Shin wane irin canji ya nuna ga rayuwar ƴan Najeriya?

Kai hatta Ƙananan masana’antu, gwamnatin Buhari daga shekara ta 2017 zuwa 2023 ta raba musu bashin da ya kai naira biliyan ɗari (N100B) ta Bankin Samar da Ci Gaba na Najeriya (DBN).

Game da bayar da takin zamani domin bunƙasawa da rage raɗaɗin talauci ga manoma, ya kamata a bibiyi Presidential Fertilizer Initiative na tsohon shugaban ƙasa Buhari, domin gudun yin takon kwaɓa. Ko da maganar samar da motocin sufuri da kuma yin amfani da man diesel mai sauƙi, ita ma wannan dabarar Shugaba Buhari ya gwada ta amma ba ta tsinana komai ba.

In dai waɗannan ne tanade tanaden wannan gwamnati, to gaskiya Shugaba Tinubu shima kamar Shugaba Buharin kenan yake, domin mun jira mu ji tsare-tsare da manufofi saɓanin na baya da ba wa mutane ƙwarin gwuiwar samun canji, musamman a yanayin halin da suke ciki.

Sabbin Ƴan Majalissar Zartarwa (Ministoci)

Ita ma fa wannan gwamnatin ta Tinubu kamar wadda ta gada ta Buhari ta ɗau tsawon lokaci kafin gabatar da sunayen ministocin, duk da kasancewar gyaran doka na kaiwa majalissa sunayensu kafin kwana talatin da rantsar da shugaban ƙasa, wanda har yanzu ba a gama kaiwa sauran mutanen ba.

Duk da wannan tsawon lokaci, sai ga shi jerin sunayen da Shugaba Tinubu ya zaƙulo don naɗasu ministoci, tamkar gauraya tsimin da ya kwana ne. Domin tarun sunayen da suke ciki, walau tsofin gwamnoni ne da suka yi mulki tare da Shugaba Buhari, wasu kuma sun riƙe muƙamai a gwamnatin da ta gabata, kusan duk tsare-tsaren da kuma gudanarwar gwamnatin baya da su aka yi.

In har ba shi Shugaba Tinubun ne ke da wani jadawali nasa ba, to zai yi wahala ta canza zani a rawar da shi Tinubun zai taka don kaiwa Najeriya gaba.

In har ba a yi dace ba fa, ƴan Najeriya su shirya da karɓar ƙaddara, domin da wuya a samu canjin da a ke fatan samu a kusa, har yanzu dai, akwai alamun sauran wahala.

alhajilallah@gmail.com

Ahmed IlallahBola Ahmed TinubuMuhammadu Buhari
Comments (0)
Add Comment