Babu Buƙatar Najeriya Ta Ƙara Shigowa Da Man Fetur Daga Wata Mai Zuwa, In Ji Dangote

Wanda ya fi kowa kuɗi a Afirka kuma Shugaban Rukunin Kamfanonin Ɗangote, Aliko Dangote ya bayyana tabbatuwar shirye-shiryen Matatar Dangote da zasu kai Najeriya ga dena shigowa da tattaccen manfetur daga wata mai zuwa.

Dangote ya kuma bayyana cewar, matatar tasa na da karfin iya wadata kasashen Afirka ta Yamma da fetur da kuma dizel da ma man amfani a jiragen sama.

Ɗankasuwar ya bayyana hakan ne a taron shekara-shekara na Shugabannin Kamfanoni na Afirka jiya Juma’a a Kigali, babban birnin Ruwanda.

Ya kuma bayyana irin cigaban da aka samu a matatar tasa wanda zai tabbatar da cewar, nahiyar Afirka ta samu wadata a fannin makamashi ba tare da dogaro da kowa ba.

Ɗangote ya ce, matatar na da ƙarfin iya bai wa ƙasashen Afirka ta Yamma man fetur, haka kuma tana da ƙarfin iya bai wa ƙasashen yankin Afirka ta Yamma da na Afirka ta tsakiya, sannan kuma tana da ƙarfin iya bai wa dukkan ƙasashen Afirka man jirgin sama har ma da fitarwa zuwa ƙasashen Brazil da Mexico.

Ya ƙara da cewar sinadaran da matatar ke samarwa a yanzu haka zasu wadatar da nahiyar Afirka ta dogara da kanta, inda ya ce a yanzu haka matatar na samar da wani mai mai kama da baƙin mai sannan tana samar sinadaran da ake amfani da su wajen yin garin sabulu.

Dangote
Comments (0)
Add Comment