Babu Gaskiya a Jita-Jitar Rashin Lafiyar Tinubu – Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yi Zazzafan Raddi

Mai taimaka wa Shugaba Bola Tinubu kan harkokin wallafa, AbdulAziz AbdulAziz, ya ƙaryata rahoton wata jaridar yanar gizo, International Centre for Investigative Report (ICIR), da ta yi zargin cewa shugaban ƙasa yana fama da rashin lafiya.

Rahoton ya ce an samu bayanai daga wasu majiyoyi cewa tawagar likitocin shugaban na shirin ɗaukarsa zuwa ƙasar waje don samun kulawar gaggawa.

ICIR ta kuma rawaito cewa Tinubu ya kwanta jinya na tsawon kwanaki, lamarin da ya hana shi halartar muhimman tarukan gwamnati.

Da yake magana da BBC Hausa a ranar Litinin, AbdulAziz ya bayyana rahoton da cewa “babu ko kaɗan daga gaskiya a cikin wannan labari; a halin yanzu shugaban na ofishinsa yana gudanar da ayyukan gwamnati.”

Mai ba da shawara na musamman ga shugaban kan labarai da dabarun ɗsu, Bayo Onanuga, ya shaida wa ICIR cewa “mutane dai suna iya gaya maka kowace irin jita-jita da ba ta da tushe.”

Ya ƙara da cewa, “yana ofishinsa jiya (yana nufin 5 ga Agusta), na ziyarce shi, kuma yana aiki.”

Onanuga ya ce akwai lokutan da shugaban zai zaɓi yin aiki daga gida ko daga ofis gwargwadon yanayi.

Wannan ƙarin haske ya zo ne a daidai lokacin da jita-jitar rashin lafiyar shugaban ke ƙara yaɗuwa a kafafen sada zumunta.

Comments (0)
Add Comment