Badaru Abubakar: Jagoran Amana da Haɗin Kai, Inji Matasan APC

Ƙungiyar Wayar da Kan Matasa da Dalibai ta Jam’iyyar APC a Jihar Jigawa ta nuna cikakken goyon bayanta ga tsohon Gwamnan jihar kuma Ministan Tsaro na yanzu, Badaru Abubakar, tana mai yabawa da kyakkyawan shugabancinsa a matsayin “mutum mai amana da da samar da haɗin kai.” 

A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Zaharradin Ahmad Aliyu, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta jinjina wa jajircewar Badaru wajen bin ƙa’idojin APC da ƙoƙarinsa na haɗa kan mambobin jam’iyyar a matakin jiha da ƙasa baki ɗaya. 

“Lokacin mulkinsa a matsayin gwamna, Badaru ya aiwatar da ɗimbin ayyukan ci gaba da suka yi daidai da tsarin mulkin APC tare da bai wa mutane muƙamai bisa ƙa’idojin jam’iyyar,” inji sanarwar. 

Ƙungiyar ta yabawa matakin kafa tarihi da Badaru ya ɗauka na bayar da shawarar fitar da Gwamnan Jigawa na yanzu daga yankin Arewa maso Gabas na jihar, wanda ta kira “babbar nasara” da ba a taɓa samun irinta ba tun farkon demokuraɗiyya a jihar. 

Haka kuma, ƙungiyar ta ƙara haskaka rawar da yake takawa a ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a matsayinsa na Ministan Tsaro, abin da ta ce yana ƙara tabbatar da kyakkyawan tarihinsa a matsayin mai samar da haɗin kai kuma jagoran mulkin gaskiya. 

Duk da jinjinawa nasarorin Badaru, ƙungiyar ta yi Allah-wadai da abin da ta kira “zarge-zargen ƙanzon kurege na ayyukan cin amanar jam’iyya” da aka yi masa. 

“Irin waɗannan zarge-zargen suna nuna ko dai rashin fahimtar tsarin mulkin jam’iyyar ko kuma fifita buƙatun kai a kan samar da alkhairin bai ɗaya,” sanarwar ta bayyana, tana kira da a samu haɗin kai a cikin jam’iyyar. 

Ƙungiyar ta yi kira ga Gwamna Alhaji Umar Namadi da ya ƙarfafa dangantaka da Badaru, tana mai jaddada muhimmancin aiki tare don ci gaban Jihar Jigawa. 

“Haɗaka tsakanin gwamnan da Ministan Tsaro zai fi amfani wa mutanen Jigawa fiye da karkatar da hankali kan masu neman damar siyasa,” a cewar ƙungiyar. 

Ƙungiyar ta sake jaddada aminta da shugabancin Badaru, tana kira ga duk masu ruwa da tsaki da su haɗa kai da shi, tana mai yabawa da jajircewarsa wajen inganta zaman lafiya, kwanciyar hankali, da nasarorin manufofin APC. 

“Muna alfahari da kasancewa tare da H.E. Badaru Abubakar, mutum mai amana, son haɗin kai, da jajircewa ga tabbatar da manufofin APC,” sanarwar ta bayyana a ƙarshe.

Badaru AbubakarGwamna Namadi
Comments (0)
Add Comment