Bankin Duniya ya sanar da cewar zai dakatar da bai wa ƙasar Uganda sabon bashi saboda dokar hana auren jinsi da ƙasar ta samar.
Bankin da ke birnin Washington ya bayyana hakan ne a jiya Talata, inda ya ce, zai dena biyan kuɗaɗen aiwatar da aiyuka a ƙasar har sai an ɗauki matakan gyara dokar tare da kare haƙƙin marassa rinjaye da kuma dena cin zarafi da nuna wariya gare su.
Bankin ya ce, dokar hana auren jinsi ta Uganda ta saɓawa manufofin Bankin Duniya na shigar da kowa cikin al’amura ba tare da la’akari da ƙabila, jinsi ko ɗabi’ar aure ba.
Ya ƙara da cewa, dokar ta saɓawa wannan ƙoƙari na Bankin, inda ya ce kawar da cin zarafi da damawa da kowa shine ginshiƙin aiyukansa a faɗin duniya.
Bankin ya kuma ce zai ƙara sanya ido domin ganin abubuwan da suke faruwa, tare da tanadin shirin kariya daga nuna ƙyama domin sanin abubuwan da ya kamata ya yi.
Tun a watan Mayu ne dai, Bankin ya ce dokar hana auren jinsin ta Uganda ta saɓawa manufofinsa, sannan kuma amfani da ita na matuƙar da damunsa.
Shugaban Bankin Duniya, Ajay Banga, wanda ya fara aiki a watan Yuni, na fuskantar ƙorafe-ƙorafe daga ƴan ƙungiyoyin fararen hula har 170 waɗanda ke neman Bankin ya dakatar da bai wa Ugandan bashi.
A watan Yuni, ƙasar Amurka ta sanya takunkumin zirga-zirga ga jami’an gwamnatin ƙasar Uganda saboda amincewa da dokar da suka yi, wadda Shugaban Ƙasar, Yoweri Museveni ya sanya wa hannu.
Museveni dai ya bayyana ɗabi’ar auren jinsi a matsayin taɓin ƙwaƙwalwa, ya kuma yi watsi da dukkan kushen da ake yi wa dokar, wadda ya bayyana a matsayin wadda ta zama dole domin kare yaɗuwar baɗalar.