Bayan Ciyo Bashin Sama Da Naira Tiriliyan 5 Don Inganta Lafiya A Najeriya, Har Yanzu Harkar Na Taɓarɓare

Rahotanni sun nuna cewa Bankin Duniya ya amince tare da bayar da lamuni da tallafi na kiwon lafiya ga Najeriya da darajarsu ta kai dala biliyan 3.64 (N5.4 tiriliyan) cikin shekaru tara da suka gabata, amma ƙungiyoyin likitoci, ma’aikatan jinya, da shugabannin kiwon lafiya na jihohi na cewa babu wani gagarumin sauyi a asibitocin ƙasar.

Ƙididdiga daga shafin ayyukan Bankin Duniya sun nuna cewa an amince da aƙalla manyan ayyukan kiwon lafiya guda 11 daga 2016 zuwa 2025, amma duk da haka cibiyoyin lafiya da dama na fama da ƙarancin wutar lantarki, magunguna, da kayan aiki.

Shugaban Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙarin Ƙwarewa (NARD), Dakta Tope Osundara, ya bayyana cewa: “In da wannan kuɗi yana nan, da mun ga babban ci gaba… amma ka je asibiti a wasu lokuta, babu magani, babu wuta.”

Ƙungiyar MDCAN ta ce duk da wasu sabbin gine-gine, samar da horo da samun ƙwararrun ma’aikata na ci gaba raguwa.

Kakakin Ƙungiyar Ma’aikatan Jinya na Tarayya, Omomo Tibiebi, ya ce Najeriya na da ɗaya daga cikin mafi ƙasƙancin tsawon rayuwa a duniya – shekaru 54 – tare da mace-macen iyaye mata da yara ƙanana masu yawa, duk da lamunin da ya haura dala biliyan 3.

Masana sun ce kashi 16% kacal na kuɗin da aka amince da shi aka fitar har zuwa watan Yulin 2024, abin da ke haifar da shakku kan saurin aiwatar da ayyuka.

Haka kuma, an gano cewa bashin Najeriya ga Bankin Duniya ya ƙaru zuwa dala biliyan 18.23 a farkon 2025, inda yake da kusan kashi 40% na dukkan bashin da ake bin Najeriya daga ƙasashen waje.

Yayin da gwamnati ke neman ƙarin tallafin waje, ƙwararru na gargaɗin cewa sai an tabbatar da gaskiya, bin-diddigi, da alfanu mai tasiri kafin kuɗaɗen su zamo wani sabon nauyi ga ƴan ƙasa.

Comments (0)
Add Comment