Bayan Karɓar Maƙudan Kuɗin Fansa, Ƴan Bindiga Sun Halaka Wani Shugaban APC

Al’umma da iyalan Nelson Adepoyigi, shugaban jam’iyyar APC na mazaba ta biyar a ƙaramar hukumar Ose ta jihar Ondo, na cikin damuwa da baƙin ciki bayan tabbatar da cewa ƴan bindigar da suka yi garkuwa da shi sun kashe shi duk da biyan kuɗin fansa da aka tara.

Rahotanni sun nuna cewa, an baiwa ƴan bindigar naira miliyan biyar da kayan abinci domin samun ƴancin shugaban jam’iyyar, amma maimakon su sako shi, sai suka yi garkuwa da mutane biyu da suka kai kuɗin, suka kuma buƙaci ƙarin naira miliyan 30 kafin su sako su.

A cewar wani babban jigo na garin Ifon da ya nemi a ɓoye sunansa, har yanzu ba a gano gawar mamacin ba amma waɗanda suka je da kuɗin sun dawo gida lafiya daga baya.

Shugaban ƙaramar hukumar Ose, Clement Ojo, ya tabbatar da aukuwar lamarin yana mai cewa, “Gaba ɗayan shugabanni da al’ummar ƙaramar hukumar Ose na cikin alhini bisa wannan mummunan lamarin. Mun miƙa ta’aziyyarmu ga iyalai, abokai da ƴan siyasar da suka yi aiki da marigayin.”

WANI LABARIN: Cikin Mako 3, Kusan Kullum Sai Boko Haram Ta Kai Hari A Borno, Yayin Da Ƴan Jihar Ke Ƙara Tsunduma Gudun Hijira

Sai dai bai bayyana yadda aka tabbatar da rasuwar Nelson ba, ko kuma ko an sake biyan ƙarin kuɗin fansar daga baya.

“Mun shiga matakin haɗari matuƙa saboda yawaitar satar mutane da har yanzu ba mu ga cikakken tsaro ba,” in ji Ojo, yana mai cewa kafin aukuwar wannan lamarin, wani mazaunin yankin ya kuɓuta da kyar daga ƙoƙarin sace shi a ƙofar gidansa.

Ya ce lamarin ya ɗauki sabon salo, inda ƴan bindigar ke kai farmaki ba tare da tsoro ko ɓoyewa ba, har ma suna sace mutane a cikin gida ko a kan hanya.

Ojo ya buƙaci hukumomin tsaro su gaggauta tura jami’an tsaro da na’urorin tsaro zuwa yankunan da abin ke faruwa, tare da neman kyakkyawan haɗin gwiwa da al’umma domin shawo kan matsalar.

“Dole ne a kama masu hannu a wannan kisan gillar da kuma gurfanar da su domin ya zama izina ga wasu,” in ji shi.

A nasa martanin, Kwamishinan ƴan sandan jihar Ondo, Olutokunbo Afolabi, ya ce ba su tabbatar da mutuwar Adepoyigi ba tukuna, amma tuni sun tura jami’ai na musamman zuwa Ifon domin gudanar da bincike.

Lamarin ya sake jefa jama’a cikin fargaba game da irin hatsarin da ke tattare da matsalar tsaro da ke ƙara ƙamari a yankin kudancin Najeriya.

Comments (0)
Add Comment