Bello Turji Ya Amince Ya Rage Kuɗin Fansa Daga Naira Miliyan 50 Zuwa Naira Miliyan 30

Mutanen garin Moriki a Ƙaramar Hukumar Zurmi ta jihar Zamfara sun samu nasarar shawo kan sanannen jagoran ƴanta’adda, Bello Turji, inda ya rage kudin fansar da ya ɗora musu daga naira miliyan 50 zuwa naira miliyan 30, tare da ba su wa’adin ranar Laraba don biyan kuɗin.

Jaridar DAILY POST ta gano cewa wannan kuɗi yana a matsayin kuɗin diyya ne saboda kashe shanun Turji da sabon kwamandan sojojin da ke sansanin soja a Moriki ya yi.

An buƙaci kowane mai gida ya biya naira 10,000, yayin da aka umurci matasa marasa aure da su biya naira 2,000 domin a haɗa kuɗaɗen.

An kuma gano cewa mazauna garin suna cigaba da biyan kuɗin duk da shawarar kwamandan sojojin ta kada su biya, tare da alƙawarin cewa ba zai sake cutar da dabbobin Turjin ba.

Mazauna garin, kamar yanda DAILY POST ta gano, suna tsoron cewa idan suka gaza biyan kuɗin, Turji zai sake kai musu hare-hare na ta’addanci, kuma ba wanda zai iya kare su daga azabtarwarsa.

Jaridar DAILY POST ta kuma gano cewa kusan ƴan siyasa da masu rajin kare haƙƙin farar hula goma sha biyar suna hannun Turji a matsayin waɗanda yai garkuwa da su, bayan da aka sace su daga cikin Moriki duk da kasancewar sojoji a cikin ƙauyen.

Bello TurjiJihar ZamfaraMatsalar Tsaro
Comments (0)
Add Comment