Gwamnan Jihar Anambra, Charles Soludo ya ce, gwamnoni zasu yi duba ga hukuncin Kotun Ƙoli wanda ya bai wa ƙananan hukumomi ƴancin tasarrufi da kuɗaɗensu.
Soludo ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis bayan ganawa da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda ya kuma bayyana hukuncin Kotun Ƙolin a matsayin babban hukunci.
Ya ce, Kotun Ƙoli ita ce ƙarshe wajen fassara doka, saboda haka duk lokacin da ta bayyana hukunci to ya tabbata.
Soludo ya kuma ƙara da cewa, a daren na jiya, gwamnoni zasu zauna domin tattauna yanda zasu tafiyar da sabon tsarin, inda ya kuma jaddada cewa, hukuncin Kotun Ƙolin zai bayar da damar aiwatar da adalci.