Binani Ta Musanta Zargin Cewa Ta Bayar Da Cinhancin Biliyan 2 Don Ta Ci Zabe

‘Yar takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan Jihar Adamawa da ya gabata, Sanata Aishatu Dahiru, wadda aka fi sani da Binani, ta musanta zarge-zargen da ake mata na cewa ta baiwa wasu jami’an Hukumar Zabe mai Zamanta Kanta ta Kasa, INEC, ciki har da Kwamishinan INEC na jihar cinhanci domin su bayyana ta a matsayin wadda ta lashe zaben gwamnan Jihar Adamawa.

A ranar Lahadin da ta gabata ne dai, Kwamishinan INEC na jihar ya kwace damar Jami’in Tattara Sakamakon Zaben Gwamnan jihar, inda ya sanar da Binani a matsayin wadda ta lashe zaben da ba a kammala tattara sakamakonsa ba, abin da kuma ya jawo hukumar INEC ta dakatar Kwamishinan tare da bukatar ‘yansanda su bincike shi.

‘Yan awanni bayan waccan sanarwar da ta saba ka’ida wadda Kwamishinan ya yi, wani faifan bidiyo ya dinga kafafen sadarwa na zamani, inda ake nuna Kwamishinan yana amsa cewar ya karbi cinhancin naira biliyan biyu domin ya sanar da Binani a matsayin wadda ta lashe zaben.

A bidiyon dai an nuna Ari ne rabi tsirara, bakinsa duk jini yana magana bayan an nuna masa bakin bindiga.

To sai dai kuma, a wani jawabi da Binani ta saki a ranar Talata, ta musanta cewa ta baiwa wani cinhancin naira biliyan biyu domin ya bata tsarin tafiyar demokaradiyya.

Ta yi zargin cewa, wani jami’in DSS ya yi babban kuskure wajen dora mummunan zargi a kanta.

Jawabin n a Binani ya ce, “BAN TABA YI BA, kuma ba zan taba yin haka ba. Wannan ya nuna cewa, maganar an yi tane a lokacin da aka azabtar da jami’in, aka kuma nuna masa bindiga daga bangaren mutanen Gwamnan Jihar Adamawa da kuma ‘yansandan Gidan Gwamnati da ma ‘yan bangar siyasarsu.

“Ina so na tabbatar da cewar ni mai goyon bayan demokaradiyyace, ko yaushe ina goyon bayan tsarin demokaradiyya kuma ba zan taba yin wani abu da zai rusa demokaradiyya ba. Ni ba ‘yar siyasar ko-a-mutu ko ai rai ba ce. A baya na ci zabubbuka zuwa Majalissar Wakilai da ta Dattawa ta hanyar ingantaccen zabe.

“Abin da ya faru a Adamawa wani yunkuri ne na kwace damar al’umma. Wasu kwamishinonin INEC biyu daga Abuja ne suka bukaci Kwamishinan INEC na Adamawa ya sauka da mukaminsa lokacin da suka kawo ziyarar aiki Adamawa. Wani abin zargin ma shine, ziyarar da wasu jami’an INEC na kasa suka kai Gidan Gwamnatin Adamawa da daddare, da kuma sanar da cewa sun karbe damar sanar da sakamakon zaben su da Jami’in Tattara Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar wanda shi Gwamnan Adamawa da kansa ya zaba.

“Tsoma bakin wadannan jami’an INEC daga Abuja, da kuma hakikanin yunkurin su biyun ga Gidan Gwamnati ya kamata ya zama wani abu da duk masu goyon bayan demokaradiyya zasu sa ido a kai.

“Ina kira ga duk masu goyon bayan demokaradiyya da su nuna matukar goyon bayansu ga tsarin demokaradiyyarmu ba kawai a Adamawa ba, a a, a duk fadin Najeriya ma.

“Haka kuma, kirana ga duk magoya bayana da ke Adamawa da wajen Adamawa, ina amfani da wannan dama wajen gode muku game da goyon bayanku a tsaka da nuna rashin gaskiyar da ake da farfagandar ‘yan adawa.”

AdamawaBinani
Comments (0)
Add Comment