Wani Malamin addinin Musulunci, Alhaji Yahaya Nafiu, ya yi iƙirarin cewa matarsa ta ɗauki ciki na tsawon shekaru uku da rabi kafin ta haifi yara 11 a Jamhuriyar Benin.
Alhaji Nafiu ya ce matarsa, Chognika Latoyossi Alake, ta haifi yara shida (maza biyar da mace daya) a ranar 6 da 7 ga watan Yuli, 2024, sannan ta sake haifan wasu maza biyar a ranar 14 ga Agusta, inda biyu daga cikin yaran suka rasu.
Malamin ya ce wannan ciki na musamman ya biyo bayan shakarun da matarsa ta kwashe ba tare da haihuwa ba, wanda ya kai tsawon shekaru tara kafin ta samu wannan cikin.
Bincike ya nuna cewa cikin mace ya saba daukar tsawon makonni 40, ko kuma watanni tara da rabi, kuma masana sun ce ba zai yiwu ba a ce mace ta ɗauki ciki sama da shekara guda.
Wani likitan mata, Dr James Odofin, ya bayyana cewa ba zai yiwu ba a ce mace ta ɗauki ciki na tsawon shekaru, domin aikin mahaifar da ke ba jariri abinci yana raguwa bayan watanni goma na daukar ciki.
Dr Odofin ya ƙara da cewa wasu matan na iya yin tunanin suna ɗauke da ciki saboda rashin ganin al’adarsu na tsawon watanni, duk da cewa ba su ɗauke cikin.
Dr Egbogu Stanley, wani ƙwararren likitan mata, ya ce duk wani iƙirari na cewa ciki ya wuce watanni tara ba gaskiya ba ne, domin jaririn zai mutu ne idan ya wuce wannan lokaci a cikin mahaifa.
Ya ƙara da cewa, idan aka binciki asibitin da aka ce an haihu a ciki, za a ga cewa labarin an ƙirkira ne kawai, domin ba zai yiwu a ce ciki ya haura watanni goma ba tare da an haife shi ba.
Likitan ya ce idan jariri ya wuce watanni goma a mahaifa, zai mutu, kuma likita ba zai bari ciki ya wuce wannan lokacin ba, zai yi tiyata ne ko kuma ya bayar da sinadaran da za a haife shi da wuri don gujewa matsala.