Boko Haram Sun Hallaka Sojoji A Harin Da Suka Kai Wa Rundunarsu A Yobe

Aƙalla sojoji huɗu ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da ake zargin ƴan ƙungiyar Boko Haram ne suka kai hari wa sansanin sojoji na 27 Task Force Brigade da ke Buni Yadi, ƙaramar hukumar Gujba a Jihar Yobe.

Wannan hari ya zo ne ƙasa da sa’o’i 24 bayan taron gwamnonin Arewa maso Gabas a Damaturu, inda suka amince da sabbin dabaru na yaƙi da ta’addanci a yankin.

Wani jami’in tsaro da ya tsira daga harin ya shaida wa DAILY TRUST cewa ƴan ta’addar sun kai harin ne da misalin ƙarfe 2 na dare, inda suka ƙona kayan yaƙi da dama, suka kuma kashe sojoji huɗu, duk da cewa “mun tsaya tsayin daka kuma mun yi musayar wuta da su.”

Hedikwatar sojojin Najeriya ta tabbatar da faruwar harin a shafinta na Facebook, tana mai cewa “dakarun Operation Hadin Kai na ci gaba da yaƙi da ISWAP a Buni Gari, Jihar Yobe, Cikakken bayani zai biyo baya,” kamar yanda TIMES NIGERIA – HAUSA ta rawaito a jiya.

WANI LABARIN: Bayan Mutuwar Wanda Ake Zargi A Bauchi, Wasu Ƴansanda Uku Sun Shiga Hannu

Sai dai har zuwa lokacin da ake kammala haɗa wannan rahoton, ba a fitar da ƙarin bayani kan adadin sojojin da suka mutu ko na ƴan ta’addar ba.

Buni Yadi, wanda ke da nisan kilomita 65 daga Damaturu, shi ne garin Gwamna Mai Mala Buni, kuma harin ya tilasta wa mazauna da dama barin gidajensu zuwa inda suka fi aminta.

Har ila yau, dakarun soji sun rufe babbar hanyar da ke haɗa Yobe da Biu da sauran sassan Kudancin Borno, sakamakon harin.

Yankin ya daɗe yana fama da hare-haren da Boko Haram ke kai wa sansanonin soji da al’ummomi, ciki har da Sabon Gari, Wajiroko da Wulgo, inda suka ƙwace makamai da kashe dakarun tsaro, lamarin da ya sa Gwamna Zulum da Shehun Borno da sauran ƴan majalisar dokoki na ƙasa da na jihohi suka buƙaci gwamnati ta ɗauki matakin gaggawa.

Comments (0)
Add Comment