A ƙalla mutane huɗu ne suka mutu bayan harin ƴan Boko Haram a Dalori Gari, Konduga, Jihar Borno, yayin da suke rakiyar manoma.
An ce waɗanda suka rasun sun haɗa da wani memba na Civilian Joint Task Force, wani maharbi, soja da wani ɗansanda.
Majiyoyi na gida sun bayyana cewa “ƴan ta’addar sun ɓoye baburansu sannan suka mamaye wurin a ƙafa.”
An rawaito cewa an kai harin ne wajen da ke kusa da Jami’ar Maiduguri a safiyar Litinin.
Rahotanni sun ce akwai yiwuwar an yi garkuwa da wasu amma hakan bai tabbata ba tukuna.
Har yanzu jami’an tsaro ba su tabbatar da lamarin ba domin Kakakin ƴan sanda Nanum Keneath bai amsa kiran wayar da Premium Times tai masa ba.