Shugaban Haɗakar Ƙungiyoyin Fararen Hula ta Jihar Jigawa, Comrade Musbahu Basirka ya bayyana buƙatar ƴan ƙungiyoyin da cewa, ita ce a magance matsin rayuwar da ya addabi al’umma, cefanar da ilimi, ƙaruwar kuɗin wutar lantarki da kuma magance ambaliyar ruwa.
Musbahu Basirka ya bayyana hakan ne a jiya, lokacin da ya jagoranci ƴan ƙungiyoyin fararen hula yin zanga-zangar nuna rashin amincewa da yanayin da janye tallafin man fetur ya jawo ga ƴan Najeriya, wadda aka gudanar da a Dutse.
Basirka ya bayyana cewa, zanga-zangar ba ta siyasa ba ce, zanga-zanga ce da ta shafi ƙwalawar da ƴan Najeriyar da ba su ji ba ba su gani ba suke sha, waɗanda ba sa iya cin abinci sau ɗaya a rana.
Ya ce, kowanne ɗan’adam ya cancanci rayuwa da mutuntawa, inda ya ƙara da cewa, duk da arziƙin da Allah Ya horewa Najeriya na mutane da albarkatun ƙasa, amma wasu tsare-tsare na gwamnati da kuma ɓatagari sun zama tarnaƙi wajen samun ci gaban ƙasar.
Basirka ya jaddada cewa, kowanne ɗan’adam yana buƙatar abinci, ruwan sha, tufafi, wajen kwana da kuma samun yin bacci, amma tsadar rayuwa ta toshe dukkan wata martabar ɗan’adam a Najeriya.
Ya ƙara da cewa, tsadar kayan abinci ta yi yawa, tsadar kuɗin yin karatu a manyan makarantun gwamnati na ta ƙaruwa, sannan kuma damar samun aikin yi na ci gaba da raguwa.
Musbahu Basirka ya kuma ce, matsin tattalin arziƙi ya sanya miliyoyin ƴan Najeriya cikin talauci, a yanzu babu ƴan tsakiya a al’umma, masu kuɗi na ta ƙara kuɗi talaka kuma na ta ƙara talaucewa.
Ya yi kira da a samu sake fasalin tsare-tsaren Gwamnatin Tarayya na bunƙasa tattalin arziƙi, domin a cewarsa suna ƙara shaƙe ƴan Najeriya ne tare da ƙara durƙusar da talaka.
Ya ƙara da yin kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da kuma Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi da su dakatar da wasu daga cikin tsare-tsarensu domin talakawa da sauran ƴan Najeriya su sami sauƙin rayuwa.