CBN Ya Bayyana Dalilan Da Ya Sa Ya Ƙara Kuɗin Ruwa Zuwa Kaso 27.5%

Babban Bankin Najeriya ya danganta ƙaruwar kuɗin ruwa na MPR, da matsin lambar hauhawar farashin kayayaki, musamman karuwar hauhawar farashin kayayyakin amfani na asali saboda tsadar makamashi. 

Kwamitin Manufofin Kudi na CBN ya gudanar da taro a ranar 23 da 24 ga Satumba, 2024, don kimanta yanayin tattalin arziki da hada-hadar kudi, da kuma tantance haɗarin da ke fuskantar hasashen tattalin arziƙin Najeriya. 

Daga cikin mambobi 12 na kwamitin, 11 ne suka halarci taron. 

Muhimman matakan da aka cimma sun hada da shawarar kara tsaurara manufofin kudi, tare da kara kudin ruwa daga matsayin da yake zuwa kashi 27.5 cikin 100. 

Sauran matakan sun hada da ci gaba da rike tazarar bambancin MPR a kan +500/-100, da kuma ƙara adadin kuɗaɗen ajiya na bankuna, tare da barin matsakaicin yawan ruwa a kashi 30 cikin dari. 

Kwamitin ya bayyana damuwar cewa duk da raguwar hauhawar farashin kayan abinci a kwanan nan, yayin da gammayar hauhawar farashin kayayyakin na nan a matakin sama, wanda ke nuni da cewa matsalolin hauhawar farashin ba su ragu ba. 

Haka zalika, kwamitin ya yaba da daidaituwar farashin musayar kudaden waje a kasuwannin daban-daban, yana danganta hakan da tsauraran manufofi kan bankuna. 

A ƙarshe, CBN ya sake nanata kudirinsa na magance hauhawar farashin kaya da kuma daidaita farashin musayar kudaden waje, tare da jaddada bukatar aiki tare da hukumomin kudi don magance matsalolin tattalin arziki na yanzu.

CBN
Comments (0)
Add Comment