ChatGPT, wata fasahar kwaikwayon hankali da OpenAI ta ƙirƙira, ta fuskanci matsala mai tsanani a safiyar Alhamis, wanda ya hana miliyoyin masu amfani da ita samun damar shiga dandalin.
Masu amfani da dandalin, da suka yi ƙoƙarin shiga sun gamu da saƙo na kuskure da ke cewa: “ChatGPT ba ta samuwa a yanzu. Matsala: An gano matsalar – Muna aiki don gyara matsalar.”
Wannan matsala, wadda ta ɗauki tsawon sa’o’i fiye da uku, ta haifar da damuwa sosai ga ɗalibai da ƙwararru da ke dogaro da ChatGPT don gudanar da ayyuka daban-daban daga ayyukan makaranta zuwa ayyukan kasuwanci.
A shafin X (wanda a da ake kira Twitter), matsalar ta yi fice, inda aka rubuta fiye da saƙonni 27,000 zuwa safiyar Alhamis.
Haka zalika, Downdetector, wani dandali da ke bibiyar matsalolin sabis, ya bayyana cewa OpenAI ta karɓi rahotanni fiye da 27,000 daga sassa daban-daban na duniya.
Masu amfani da dandalin sun bayyana damuwarsu a shafukan sada zumunta, musamman waɗanda ke da ayyukan gaggawar da suke son kammalawa a kan lokaci.
Wani mai amfani, #chrsluvlanguage, ya rubuta: “Me yasa ChatGPT ta tsaya lokacin da nake buƙatar in yi aikin Turanci na?” Yayin da #jasmineeub ta rubuta: “ChatGPT ta tsaya kuma ina da jarabawa gobe.”
Wani mai amfani, #scottieshowtime, ya ƙara da cewa: “ChatGPT ta tsaya a ranar da nake da aikin ƙarshe da zan kammala.”
OpenAI ta amsa matsalar a shafin X da cewa: “Muna fama da matsala a yanzu. Mun gano matsalar kuma muna aiki don gyara ta. Muna bada haƙuri, za mu cigaba da sanar da ku!”
A yayin da ake fama da matsalar, Elon Musk’s Grok AI chatbot ya amsa da wani saƙo mai daɗaɗawa inda ya rubuta: “Sannun kowa da ƙoƙari, ina farin cikin haɗuwa da ku.”
Jawabin ya jawo martani da dama a shafin X, inda wasu suka duba yiwuwar Grok AI ya zama madadin amfani da ChatGPT a lokacin matsalar.
Bayan wasu sa’o’i, sabis ɗin ChatGPT ya dawo, inda Shugaban OpenAI, Sam Altman, ya tabbatar da dawowar ta a shafin X da cewa: “Mun dawo.”
Masu amfani sun bayyana jin daɗinsu da dawowar sabis ɗin.
Wani mai amfani, #Evinst3in, ya ce: “Na gode, Sam! Yanzu zan iya cigaba da aikina.”
Wani kuma, #Star_Knight12, ya tambaya: “ChatGPT ta dawo yanzu. Me ya jawo matsalar da ta faru?”
Wannan matsalar ta faru ne jim kaɗan bayan wata irinta da ta shafi dandalin Meta, ciki har da Facebook, Instagram, da WhatsApp, a ranar Laraba.