CIKAKKEN LABARI: Batun Karɓa-Karɓa Zai Iya Zamewa ADC Alaƙaƙai, Yayin Da Atiku, Obi Da Amaechi Ke Bayyana Son Yin Takara

Sabon ƙawancen ƴan adawar Najeriya da ke burin kifar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu a 2027 na ci gaba da ɗaukar hankulan ƴan siyasa da jama’a a faɗin ƙasar, inda jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta zama dandalin fafutukar.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi ne ke jagorantar wannan haɗin gwiwar tare da goyon bayan tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark, Uche Secondus, tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da kuma tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi.

A wajen ƙaddamar da ƙawancen ranar Laraba, David Mark ya bayyana cewa, “Muna ƙoƙarin ceton demokaraɗiyyar Najeriya daga zama mai jam’iyya ɗaya tilo.”

Sai dai masana na gargaɗin cewa, burin mutane da yankin da zai fitar da ɗan takara zai iya rushe haɗin gwiwar kafin lokacin zaɓe.

WANI LABARIN: Sauye-Sauyen Tsarin Mulki Da Majalisar Dattawa Ke Shirin Samarwa A Najeriya

Yayin da Atiku mai shekaru 78 ke ci gaba da nuna sha’awarsa, magoya bayansa suna ganin ƙwarewarsa a siyasa ta fi ta kowa.

Mr Amaechi kuwa ya tabbatar da niyyarsa tare da jaddada muhimmancin tsarin rabon iko tsakanin Arewaci da Kudu, yana mai cewa, “A 2015 na jagoranci yaƙi da PDP saboda sun karya yarjejeniya da Arewaci. Yin irin hakan rashin adalci ne.”

Ya kuma sha alwashin yin mulki na tsawon shekara huɗu kawai idan aka zaɓe shi, yana mai cewa, “Kudu sai ta gama wa’adinta, idan ba haka ba to na yi kuskure a goyon bayanta.”

Obi, wanda ya mamaye jihohi 11 a zaɓen 2023 duk da kasancewarsa na uku, ya bayyana cewa zai tsaya takara, yana mai cewa, “Zamu yi wa Najeriya shugabanci mai nagarta, iya aiki, da tausayawa.”

Shi ma ya bayyana cewa zai yi wa’adin shekara huɗu ne kawai idan an cimma yarjejeniyar, yana mai cewa, “Zan miƙa mulki a 28 ga Mayun 2031 idan hakan aka yarda.”

Amma Atiku, wanda tun 1993 ke fafutukar neman takarar shugabancin ƙasar, ba zai amince da hakan ba.

Masana kamar Farfesa Jibrin Ibrahim sun ce nasarar haɗin gwiwar tana tattare da sauƙe nauyin gudanar da demokaraɗiyyar cikin gida cikin gaskiya.

Batun yanki da addini kuwa zai iya zama silar taɓarɓarewar ƙawancen kamar yadda ya faru da PDP a 2015 da 2023.

Ko da za a miƙa tikitin takarar shugaban ƙasa zuwa kudu ko a bar shi a buɗe, kowanne mataki na da tasiri wajen nasara ko akasin haka.

Tabbas, ƙalubalen zaɓar inda shugaban ƙasa zai fito a 2027 na iya wargaza haɗin gwiwar ADC, musamman idan akasarin ƴan kudu sun ji an cuce su a tsarin fitar da ɗan takarar.

Comments (0)
Add Comment