CIKAKKEN LABARI: Kotu Ta Ba Wa Sanata Natasha Nasara Kan Akpabio, Ta Kuma Ci Tararta

A wani hukunci da kotun tarayya dake Abuja ta yanke, mai shari’a Binta Nyako ta soke dakatarwar da aka yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, inda ta bayyana dakatarwar tsawon watanni shida da Majalisar Dattawa ta yi mata a ranar 6 ga Maris a matsayin “mai tsanani kuma wadda ta wuce gona da iri.”

Duk da hakan, kotun ta ci tararta Naira miliyan biyar saboda wani rubutun barkwanci da ta wallafa a Facebook ranar 27 ga Afrilu, wanda aka bayyana a matsayin saba dokar kotu wadda ta hana bangarorin da ke cikin karar yin tsokaci a kafafen yaɗa labarai ko kafofin sada zumunta dangane da shari’ar.

“Rubutun nata ya saɓawa hukuncin da kotu ta bayar da ke buƙatar a guji tsokaci da zai iya gurɓata shari’ar,” a cewar mai shari’a Nyako.

Kotu ta umurci Natasha ta nemi afuwa ba tare da wata tantama ba a jaridu biyu na ƙasa da kuma a shafinta na Facebook cikin kwanaki bakwai domin ta “wanke kanta daga saɓa wa kotu.”

Duk da cewa kotu ta amince Majalisar Dattawa na da hurumin ladabtar da ƴaƴanta, ta bayyana dakatar da sanatar na tsawon kwanaki 181 na shekara a matsayin hana mazaɓarta wakilci a majalisa, lamarin da kotun ta bayyana a matsayin abin da ya saɓa da kundin tsarin mulki.

“Majalisa na da ikon ladabtar da mambobinta, amma hakan bai kamata ya kai ga hana mazaɓarsu wakilci ba,” a cewar hukuncin.

Natasha ta kai ƙara ne a ranar 3 ga Maris domin dakatar da binciken kwamitin ladabtarwa bayan taƙaddama da ta yi da Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, kan wajen zamanta a zauren majalisar.

Duk da cewa kotu ta hana ci gaba da binciken, majalisar ta ci gaba da dakatar da ita, wanda ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen yaɗa labarai tare da ƙorafin cin zarafinta ta hanyar fyaɗe, wanda majalisar ta yi watsi da shi har sau biyu.

Kotun ta bayyana cewa ko da yake majalisa na da ikon hukunta ƴaƴanta, bai haɗa da dakatar da su na dogon lokaci da zai hana mazaɓarsu samun wakilci ba.

Duk da haka, kotun ta tabbatar da wasu daga cikin matakan Akpabio da majalisar, ciki har da hana ta magana daga wani wajen da ba wajen zamanta ba, da kuma tura ta zuwa gaban kwamitin ladabtarwa.

Hakazalika, kotun ta ce matakin shugaban majalisar na ranar 20 ga Fabrairu na canja mata wajen zama yana kan ƙa’ida ƙarƙashin dokokin majalisar.

Wannan hukunci dai ya ƙara sanya Sanata Akpoti-Uduaghan a cikin sahun ƴan majalisar da suka yi nasarar ƙalubalantar dakatar da su a gaban kotu, kamar yadda Ali Ndume da Ovie Omo-Agege suka taɓa yi a baya.

Wannan hukunci dai ya haifar da martani daga ɓangarori daban-daban, musamman ganin yadda kotu ta jaddada haƙƙin ƴan mazaɓa da kuma bayyana iyakar ikon majalisar a cikin tsarin demokaraɗiyya.

Comments (0)
Add Comment