Cikin Mako 3, Kusan Kullum Sai Boko Haram Ta Kai Hari A Borno, Yayin Da Ƴan Jihar Ke Ƙara Tsunduma Gudun Hijira

Yayin da hare-haren Boko Haram da ISWAP suka sake rikiɗewa zuwa masu yawan gaske a wasu sassan jihar Borno, al’ummomi da dama na ci gaba da ficewa daga garuruwansu sakamakon tsoron halin rashin tsaro da ya sake dawowa fiye da yadda ake tsammani.

Cikin makonni uku da suka gabata, an samu rahotannin cewa ƴan ta’addar sun kai hare-hare har sau 12, inda suka hallaka ɗaruruwan sojoji da fararen hula a yankuna daban-daban, lamarin da ke ƙara karya ƙwarin gwiwar al’umma duk da tabbacin da manyan hafsoshin tsaro suka bayar bayan ziyarar da suka kai yankin.

Duk da cewa Ministan Tsaro, Badaru Abubakar, da abokin aikinsa ƙaramin minista, Bello Matawalle, tare da shugaban hafsoshin tsaro, Janar Christopher Musa, sun ce gwamnati za ta magance hare-haren, daga ranar 28 ga Afrilu zuwa yanzu, an kai hare-hare da dama a wurare irin su Chibok, Mobbar, Gwoza, Marte, da Gajiram.

Sojojin Najeriya sun ce sun hallaka wasu daga cikin ƴan ta’addar tare da ƙwace makamai da motocin yaƙi a cikin dajin Sambisa, amma duk da haka, fiye da fararen hula 40 ne aka tabbatar sun mutu.

A wasu hare-hare, ƴan ta’addar sun tare hanyoyi da sanya bama-bamai, kamar yadda aka gani a hanyar Gamboru-Ngala, inda mutane takwas suka mutu, sannan wasu suka jikkata, haka ma a harin Gajiram da aka hana su kaiwa ga nasara amma duk da haka an rasa rayukan sojoji huɗu a Dikwa da Rann.

WANI LABARIN: APC na Ƙara Gagarar Ƴan’adawa, Yayin da Tinubu Ke Cika Shekaru 2 A Karagar Mulkin Najeriya

A Marte, an samu hasarar sojoji bakwai da motocin yaƙin da aka ƙona da wasu da aka kwashe, yayin da a Baga kuma aka kashe manoma 15 a harin da aka kai a Jumma’ar nan, sannan a Wulgo aka ƙona gine-ginen gwamnati ciki har da makarantu da asibitoci.

Wani dattijo a Baga ya shaida cewa, “Boko Haram sun kafa ƙofofi a hanyoyin zuwa gona da zuwa kamun kifi, kuma suna kashe duk wanda ya ƙi bin dokokinsu ko ya wuce ba tare da izini ba.”

Sai dai Janar Musa ya bayyana cewa, “Mun samu sabbin makamai na zamani da sabbin dabaru da za mu shawo kan wannan annoba ta ta’addanci da su, kuma wannan matsin lamba da muke gani a yanzu, sakamakon yadda ake takurawa ƴan ta’addar a yankin Sahel ne, wanda ya sa suke sake shigowa Najeriya.”

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya buƙaci a gudanar da azumi na musamman don neman taimakon Ubangiji, yayin da ɗan majalisa Ahmad Satomi ya buƙaci a binciki gobarar da ta tashi a barikin Giwa da kuma sake shirin tsaro a yankin.

Satomi ya ƙara da cewa, “Jarumtaka da sadaukarwar sojojinmu na fuskantar ƙalubale sosai a sakamakon waɗannan hare-hare, yayin da rayuwar fararen hula ke cikin haɗari a kowane lokaci.”

Duk da fargaba da tashin hankalin da ake ciki, rundunar sojin Najeriya ta ce tana da cikakken iko da yanayin da ke faruwa, tana nan tana cigaba da kai farmaki a dajin Sambisa da sauran wurare domin wanzar da zaman lafiya.

Comments (0)
Add Comment