Akwai ƙwararren alamu da ke nuni da cewa za a samu rasa aiyukan a ɓangaren ma’aikatan gidajen mai a faɗin ƙasar nan, yayinda masu gidajen mai ke shirin rage ma’aikata saboda raguwar ciniki a gidajen dalilin tsadar man da ake ciki.
Binciken da jaridar DAILY INDEPENDENT ta gudanar a faɗin ƙasar nan ya nuna cewa, duk da cewar mafi yawan gidajen mai na samun yawan kuɗin ciniki saboda tashin farashin mai, an samu matuƙar raguwar yawaitar masu shiga gidajen domin shan mai da kuma raguwar yawan man da ake sha.
Wannan yanayi dai ya samo asali ne daga janyewar tallafin mai da gwamnatin Bola Tinubu tai a ranar farko ta fara mulkinta, abin da ya jawo hauhawar farashin man har ya kai wasu ba sa iya siya.
Motocin haya da dama sun daina zirga-zirga saboda rashin samun riba a harkokin sana’arsu, abin da ya jawo ƴan Najeriya da dama suka shiga cikin ƙarin ƙunci.
Ku Karanta Wannan: Ƙungiyoyin Ƙwadago Zasu Yaƙi Halin Matsin Da Ake Ciki A Najeriya
A wajen mafi yawan ƴan Najeriya dai, cire tallafin da akai wani abu ne da ya jawo musu matsatsi na rayuwa da rashin walwala saboda ƙaruwar tsadar sufuri, kayan abinci da sauran buƙatun yau da kullum.
Wani manajan babban gidan mai a birnin Lagos ya bayyana cewa, hukumar gidan a yanzu haka tana tattara sunaye a duk rassanta na Najeriya domin rage ma’aikata a dalilin raguwar ciniki.
Ya bayyana cewa, a yanzu ba sa samun ciniki kamar da, abin da ya sa hukumar gidajen man ba zata iya ci gaba da biyan ma’aikatan da ba sa komai ba.
Bincike a faɗin Najeriya ya nuna cewa, halin duk iri ɗaya ne a ko’ina cikin ƙasa, inda hukumomin gidajen mai da dama ke shirin rage ma’aikata saboda ƙarancin cinikin da ya jawo ba a buƙatar ma’aikatan.
Wani dillalin man a Ibadan, Seye Adi-gun, ya bayyanawa DAILY INDEPENDENT cewa yana matuƙar fuskantar raguwa ciniki idan aka kwatanta da lokutan baya kafin cire tallafi.
Ya bayyana cewa, a yanzu masu siyan man suna siyan lita 10 zuwa 20 ne kacal maimaikon lita 30 zuwa 50 a baya.
Ya ƙara da cewa, a da gidan mansa na ƙarar da man da aka kawo masa cikin kwanaki huɗu ne, amma tun da aka ƙara farashin man a cikin sati guda ma man bai ƙare ba, suna da saura da yawa.