Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya amince da bayar da naira dubu goma ga ma’aikatan jihar a matsayin tallafi duk wata.
Tallafin naira dubu goman na wata-wata an samar da shine domin domin a ragewa ma’aikata a jihar raɗaɗin cire tallafin mai da matsalolin tattalin arziƙin da hakan ya jawo.
Wannan mataki na gwamnatin jihar ya fito ne ta bakin Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan, Rafi’u Ajakaye a lokacin da ya gana da manema labarai a Fadar Gwamnatin da ke Ilorin a yau Litinin.
Ajakaye ya ce wannan tsari na tallafin naira dubu goma ga ma’aikata zai fara ne daga wannan watan na Yuli, sannan zai ci gaba har zuwa lokacin da za a fito da sabon tsarin mafi ƙarancin albashi.
Wannan ya samo asali ne shawarar da Kwamitin Bunƙasa Tattalin Arziƙi na Ƙasa ya bayar na cewa kowacce jiha ta duba hanyoyin ragewa ma’aikata radaɗin cire tallafin man da aka yi a ƴan kwanakin nan.
Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya kuma umarci ma’aikata da su ci gaba da tsarin da ake kai na rage yawan kwanakin aiki a sati ga ma’aikaci daga kwanaki 5 zuwa kwanaki 3 domin a ƙara sauƙaƙawa ma’aikatan a fannin kashe kuɗin sufuri.