DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin Kano Ta Hana Private Schools Ƙarin Kuɗin Makaranta

Gwamnatin Kano ta tabbatar da dakatar da ƙarin kuɗin makaranta da makarantu masu zaman kansu na jihar ke ƙoƙarin yi.

Sannan gwamnatin ta umarci dukkan makarantun da su sabunta lasisinsu domin su dace da tsarin inganta ilimi na gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf.

Gwamnatin dai ta bayyana hakan ne bayan, Baba Umar, Mai Bayar da Shawara na Musamman kan Makarantu Masu Zaman Kansu ga Gwamnan Kano ya gana da masu makarantun.

KARANTA WANNAN: BUK Ta Samarwa Ɗalibanta Aikin Da Zasu Na Samun Naira 15,000 Duk Wata

Baba Umar ya ce, dakatar da ƙarin kuɗin makarantar da makarantun ke yunƙurin yi, an zo da shi ne domin kare haƙƙin kowa.

A yanzu haka dai makarantun jihar Kano na cikin hutu, yayin da masu makarantun ke shirin dawowa a karo na farko bayan kayan masarufi sun yi matuƙar tashi a Najeriya saboda janye tallafin man fetur.

Sai dai kuma da alama wasu masu makarantun da iyayen yaran na ganin baiken hukuncin na gwamnatin.

Jihar Kano
Comments (0)
Add Comment