DA ƊUMI-ƊUMI: Kamfanin BUA Ya Sauƙo Da Farashin Simintinsa Zuwa Naira 3,500

Kamfanin yin siminti na BUA ya sanar da rage farashin simintinsa mai nauyin kilogram 50 daga naira 4,800 zuwa naira 3,500 daga gobe Litinin.

Kamfanin ya sanar da rage farashin ne a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a yau Lahadi.

Kamfanin ya ce, la’akari da bayanan da yai a baya na niyyar rage farashin simintinsa bayan kammala aikin faɗaɗa kamfanin a ƙarshen shekara don bunƙasa samar da ababen more rayuwa, hukumar gudanarwar kamfanin ta na sanar da abokan hulɗarsa da al’umma baki ɗaya cewar ya sauƙo da farashin buhun simintin daga ranar 2 ga watan Oktoba, 2023.

ƘARIN LABARI: JERIN SUNAYE: Masu Degree Da Suka Samu Aikin Sa Kai Na J-Teach A Jigawa

Kamfanin ya ce ya yanke shawarar sauƙo da farashin ne tun yanzu domin farantawa abokan hulɗarsa inda a yanzu zasu dinga siyan kowanne buhu ɗaya a kan naira 3,500.

Kamfanin ya kuma ce, idan ya kammala aikin sabbin guraren samar da simintinsa da ya ke, wanda zai sa kamfanin fitar da simintin da ya kai tan miliyan 17 a shekara, zai ƙara sauƙo da farashin ƙasa a farkon shekarar 2024.

Duk waɗanda suka yi odar simintin a tsohon farashi, za a daidaita cinikin da sabon farashin da zai fara aiki gobe, in ji kamfanin.

BUAFarashin Siminti
Comments (0)
Add Comment