DA ƊUMI-ƊUMI: Kotu Ta Bayar Da Belin Emefiele A Kan Naira Miliyan 20

Dakataccen Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya samu beli a yau Talata a kan naira miliyan 20 da kuma kadara mai kwatankwanci wannan kuɗi daga Babban Kotun Tarayya da ke Jihar Lagos.

An ba da belin nasa ne bayan ya bayyana cewa bai aikata laifuka biyun na mallakar makamai ba bisa ƙa’ida da ake zarginsa da su ba.

Karanta Wannan: An Kori Malaman Jami’a Biyu Saboda Zargin Aikata Baɗala

Emefiele na fuskantar tuhume-tuhume guda biyu da suka haɗa da mallakar bindiga da harsasai ba bisa ƙa’ida ba wanda Ma’aikatar Shari’a ta Ƙasa ta gabatar a gaban Alƙali Nicholas Oweibo.

Ma’aikatar Shari’ar na ƙarar Emefiele ne kan mallakar ƙaramar bindiga (JOJEFF MAGNUM 8371) ba tare da lasisi ba.

Sannan kuma ana zarginsa da mallakar harsasai masu hatsari ba tare da lasisi ba.

Godwin EmefieleKotu
Comments (0)
Add Comment