DA ƊUMI-ƊUMI: Sanatoci Sun Cire Sunan El-Rufa’i Da Wasu Mutum Biyu Daga Ministocin Tinubu

Sunan tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi ɓatan dabo a cikin jerin sunayen ministocin da sanatoci suka tabbatar a yau Litinin.

Haka kuma a cikin sunayen ba a ga sunan Sanata Abubakar Danladi daga Jihar Taraba ba da kuma na tsohuwar Shugabar Bankin Nexim, Stella Oketette daga Jihar Delta.

Sanatocin bayan ɗebe tsawon mako guda suna tantance ministocin sun amince tare da tabbatar da mutane 45 cikin mutane 48 da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya tura musu.

TASKAR YANCI ta rawaito cewa, lokacin tantancewar, tsohon gwamnan Kaduna, El-Rufai ya fuskanci ƙalubale daga Sanatan Kogi ta Yamma, Sunday Karimi.

Bayan El-Rufai ya kammala gabatar da kansa gaban majalissar sanatocin ne, Karimi ya tashi ya ce yana da ƙorafin da aka rubuta a kan El-Rufai game da matsalolin tsaron da suke faruwa a yankin Kudancin Kaduna.

Karimi ya ce ƙorafin da yake tattare da shi a kan El-Rufai ya shafi matsalolin tsaro, zaman lumana da haɗin kan Najeriya.

Karimi ya miƙa takardun ƙorafin da ya nunawa majalissar ga Mataimakin Shugaban Majalissar Dattawa, Sanata Barau Jibrin domin dubawa.

Haka shi ma, Sanata Danladi daga Jihar Taraba, PUNCH ta gano cewar akwai umarnin kotu da ya hana shi riƙe wani muƙamin gwamnati na tsawon shekaru goma.

Ita kuma Okotette akwai zarge-zargen rashin bin ƙa’idojin aiki a tare da ita, ciki har da rashin bayyana kadarorinta a lokacin da take shugabancin Bankin Nexim.

Nasir El-Rufa'i
Comments (0)
Add Comment