Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai yi wa ƴan ƙasa jawabi yau Litinin 31 ga watan Yuli, 2023 da misalin ƙarfe 7 na dare.
Mai Magana da Yawun Shugaban Ƙasa, Dele Alake ne ya sanar da hakan a safiyar yau.
Alake ya yi kira ga gidajen talabijin, radio da sauran kafafen yaɗa labarai da su jona da Hukumar Gidan Talabijin da Radio ta Najeriya domin yaɗawa ƴan ƙasa jawabin.
Sanarwar ba ta bayyana batutuwan da shugaban zai yi magana a kai ba, sai dai akwai barazanar shiga zanga-zangar gama gari a ƙasar wadda Ƙungiyar Ƙwadago ta NLC ta shirya farawa ranar Laraba mai zuwa kan janye tallafin man fetur.
Bayan sanar da yin zanga-zangar ne aka jiyo Shugaba Tinubu yana roƙon ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri, su ƙara masa lokaci kafin ya daidaita al’amura.
NLC dai ta jaddada ƙudirinta na gudanar da zanga-zangar duk barazanar cewar aiwatar da hakan zai iya zama saɓawa kotun ma’aikata da ta dakatar da ita daga shiga yajin aiki.