Rayuwar hanɓararren Shugaban Ƙasar Nijar, Mohammed Bazoum na cikin hatsari saboda barazanar da waɗanda suka hamɓarar da shi kuma suke riƙe da shi suka yi, ta cewar zasu kashe shi matuƙar ECOWAS tai ƙoƙarin tura sojoji don su dawo da mulkinsa.
Sojojin Nijar da suka jagoranci juyin mulkin sun bayyana wannan aniya ta su ne, ga wata babbar jami’ar diflomasiyya ƴar ƙasar Amurka, yayinda wasu manyan jami’an Turawa su biyu suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP labarin a jiya Alhamis da daddare.
Wannan barazana dai na zuwa ne a daidai lokacin da ƙungiyar ECOWAS ta yanke shawarar yin amfani da ƙarfin soji wajen dawo da mulkin demokaraɗiyya a Nijar, biyo bayan turjiyar da sojojin da suka yi juyin mulki a ƙasar suka nuna.
Da yake magana a yanayin da ba ya so a bayyana sunansa saboda ƙarfin maganar, wani babban jami’in soja na Turawa ya ce, wakilin masu juyin mulkin ya shaidawa Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka, Victoria Nuland barazanar da ke kan Bazoum a ranar Litinin, lokacin da ta kai ziyara ƙasar.
Kamfanin AP ya bayyana cewar, wani babban jami’in ƙasar Amurka ya tabbatar da barazanar, a yanayi na ɓoye kai saboda bai samu izinin bayyana lamarin ga manema labarai ba.
Bazoum dai, wanda aka hamɓarar a ranar 26 ga watan Yuli, yana ci gaba da kasancewa a hannun waɗanda suka yi masa juyin mulkin har kawo yanzu.
Haka kuma, a ɓangaren ECOWAS, da suke kammala taron da suka gabatar a jiya kan ƙasar Nijar, Shugaban Gudanarwa na Ƙungiyar, Omar Touray ya ce, ƙungiyar ta bayar da umarnin tura sojoji da suke jiran ko-ta-kwana domin su dawo da mulkin demokaraɗiyya a Nijar.
Sai dai kuma Touray bai bayar da cikakken bayani kan yanda kai harin zai kasance ba da kuma lokacin da za a fara.