DA ƊUMI-ƊUMI: Ƴan Majalissar Wakilai Na Neman A Mayar Da Wa’adin Shugaban Ƙasa Shekaru 6

Wani gungun ƴan majalissar wakilai na neman a gyara Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 domin bayar da damar zagaya muƙamin shugaban ƙasa zuwa yankuna 6 na Najeriya.

Ƴan majalissar na kuma son a samar da wa’adi ɗaya na shekaru 6 ga shugaban ƙasa da gwamnoni.

Da yake magana a madadin ƴanmajalissun yau Litinin a Abuja, ɗan majalissar wakilai mai wakiltar mazaɓar Ideato ta Kudu/Ideato ta Arewa, daga Jihar Imo, Ikenga Ugochinyere ya ce, “Rage kashe kuɗaɗen gudanar da gwamnati da asarar da ake yi, samun ingancin tafiyar da gwamnati, da daidaiton ƙasa ta hanyar samar da wa’adin shekaru 6 sau ɗaya ga shugaban ƙasa da gwamnoni zai matuƙar temakawa wajen matakan rage kashe kuɗaɗe.”

Comments (0)
Add Comment