DA ƊUMI-ƊUMI: Ƴan Sanda Sun Ayyana Baturen Birtaniya Da Ɗan Najeriya a Matsayin Wadanda Ake Nema Bisa Yunƙurin Kifar Da Gwamnatin Tinubu

Rundunar ‘Yansandan Najeriya, a ranar Litinin, ta bayyana wani ɗan ƙasar Birtaniya mai suna Andrew Wynne, wanda kuma aka sani da Andrew Povich, da wani dan Najeriya mai suna Lucky Obiyan, a matsayin wadanda ake nema saboda zargin yunkurin kifar da gwamnatin da aka zaba ta dimokuradiyya a kasar.

Ƴansandan sun zargi ɗan kasar Birtaniya da gina wani tsarin ƙungiyar asiri domin kifar da gwamnati da jefa ƙasa cikin rikici.

Da yake yi wa manema labarai jawabi a Abuja, mai magana da yawun rundunar, Muyiwa Adejobi, ya ce Wynne ya kama wani wuri a Gidan Ƙwadago (Labour House) sannan ya kafa wata makaranta a matsayin rufa-rufa.

Ya ce, “Rundunar ‘Yansandan Najeriya ta kaddamar da cikakken bincike kan ayyukan wani ɗan ƙasar waje da kuma wasu gungun masu son tayar da zaune tsaye a Najeriya ta hanyar sauya gwamnatin da aka zaɓa ta dimokuradiyya, da kuma kitsa tashin hankali a fadin kasar.

“Bayan gudanar da tattara bayanai na sirri da hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro, an kama mutane tara da suka samu gudunmawar kudi mai yawa daga wasu kasashen waje don tada zaune tsaye a kasar.

“Sakamakon binciken farko ya nuna cewa sun kitsa da kuma daukar nauyin zanga-zangar tashin hankali, yada bayanan karya, da kuma aikata wasu ayyuka na karya doka domin haifar da fitina da kuma neman amincewa da shirinsu na kifar da gwamnatin da aka zaba ta dimokuradiyya.

“Bincike ya gano wani sojan haya na kasashen waje mai suna Andrew Wynne (wanda aka fi sani da Andrew Povich ko Drew Povey), dan kasar Birtaniya, wanda ya gina tsarin kungiyar sirri domin kifar da gwamnati da kuma jefa kasar cikin rikici. Ya kama wuri a Gidan Kwadago, Abuja, don bude wata kasuwar littattafai mai suna ‘Iva Valley Bookshop’ da kuma kafa wata makaranta mai suna ‘STARS of Nations Schools’ a matsayin rufa-rufa domin aikata wannan barna.”

Adejobi ya ce, akwai shaidun rubutattun bayanai da kuma amsoshin da suka nuna cewa Wynne ne ya bayar da kudade da kuma jagorancin ayyukan domin kifar da gwamnati ta hanyar da ba ta dace ba.

Ya ce, “Shaidun rubutattun bayanai da kuma amsoshin sun nuna cewa Andrew Wynne ne ya bayar da umarni, yana lura da cigaban ayyukan, da kuma bayar da kudade da jagorancin ayyukan domin cimma burin sauya gwamnati ba bisa ka’ida ba a Najeriya.

“Ya tara tare da raba biliyoyin nairori ga abokan huldarsa na Najeriya, yana umartar su da su shirya jama’a domin su kai hari kan ofisoshin ‘yansanda da barikin soja, suna tsammanin zubar da jini da zai haifar da Allah wadai daga kasashen duniya game da gwamnatin Najeriya. Wadannan ayyukan sun sabawa doka ta Hana Ta’addanci (Prevention Act) ta shekarar 2011 da kuma sauran dokoki masu nasaba,” in ji mai magana da yawun rundunar ‘yansanda.

Adejobi ya ce Wynne da babban abokin aikinsa, Obiyan, sun tsere daga kasar.

Ya ce, “Tun bayan fara gudanar da bincike, Andrew Wynne ya tsere daga kasar. Shi da babban abokin aikinsa a gida, mai suna Lucky Ehis Obiyan, an bayyana su a matsayin wadanda ake nema, kuma an fara neman su a duk fadin duniya da nufin tsare su saboda binciken da ake yi a kansu.”

Zanga-Zanga
Comments (0)
Add Comment