DA ƊUMI-ƊUMI: ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki

Ƙungiyar Malam Jami’o’i ta Ƙasa, ASUU, biyo bayan Taron Shugabanninta na Ƙasa da ta yi a Jami’ar Maiduguri ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ofishin Babban Akawunta na Tarayya da ta saki kuɗaɗen ariyas na ƙarin girma da mambobin ƙungiyar ke bi don a samu zaman lafiya da nutsuwa a jami’o’in Najeriya.

A wata sanarwa da ASUU ta saki a yau Alhamis da safe, ƙungiyar ta ce, ta damu da bayanan da su ke fitowa kan badaƙalar ɗaukar aiki da aka yi a Najeriya ta hanyar amfani da tsarin biyan albashi na IPPIS.

KARANTA WANNAN: BUK Ta Samarwa Ɗalibanta Aikin Da Zasu Na Samun Naira 15,000 Duk Wata

ASUU ta ce, mambobinta na bin kuɗaɗen ƙarin girma na watanni da dama, sannan kuma ƙoƙarinta na a sasanta ta ofishin Babban Akawunta na Tarayya ya ci tura.

Ƙungiyar ta ce, matuƙar gwamnati tana so ta kuɓutar da jami’o’in daga tsunduma yajin aiki da rashin samun nutsuwa, to ta gaggauta sakin kuɗaɗen ƙarin girman da ake bin ta.

Haka kuma, ASUU ta ce, ta yi watsi da dukkan wani ɗaukar aiki ko naɗe-naɗen da aka yi ba bisa ƙa’ida ba a jami’o’in Najeriya ta hanyar tsarin IPPIS a jami’o’in Najeriya.

ASUUYajin Aiki
Comments (0)
Add Comment