DA ƊUMI-ƊUMI: DSS Ta Kama Shugaban NLC, Joe Ajaero

Jami’an Hukumar Tsaro ta DSS sun kama Shugaban Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajaero.

An kama Ajaero ne a safiyar yau Litinin a filin jirgin sama na kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Ingila.

Shugaban NLC ɗin zai je halartar taron kungiyar ma’aikata ta TUC a birnin Landan wanda da za a fara yau.

Bayanai kan dalilan kama shi ba su fito fili ba a lokacin da aka samu wannan labarin.

DSSNLC
Comments (0)
Add Comment