DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnati Na Tattaunawa Da Ƴan Ƙwadago A Fadar Shugaban Ƙasa Don Dakatar Da Yajin Aiki

Gwamnatin Tarayya da haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƴan ƙwadago na tattaunawa a sirrance a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Tattaunawar ta gaggawa ta yau Lahadi wadda gwamnati ta kira, na zuwa ne a matsayin yunƙuri na ƙarshe na kare tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani wanda Ƙungiyar Ƴan Ƙwadago, NLC, da Ƙungiyar Ƴan Kasuwa, TUC, suka shirya farawa a ranar Talata mai zuwa.

Waɗanda ke wakiltar ɓangaren ƴan ƙwadago a wajen zaman sun haɗa da, Shugaban Ƙungiyar NLC, Joe Aajero; Sakataren Ƙungiyar TUC, Nuhu Toro da kuma Sakataren Ƙungiyar NLC, Emma Ugbaja.

Tawagar ɓangaren Gwamnatin Tarayya kuma na ƙarƙashin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila.

Sauran wakilan gwamnati a wajen zaman sun haɗa da Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Dr. Folasade Yemi-Esan; Mai Bayar da Shawara kan Harkokin Tsaro na Ƙasa, Nuhu Ribadu; Ministan Ƙwadago da Samar da Aikin Yi, Simon Lalong; Ƙaramin Ministan Ƙwadago da Samar da Aikin Yi, Nkeiruka Onyejecha; Ministan Kuɗi, Wale Edun; Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziƙi, Atiku Bagudu da kuma Ministar Harkokin Jin Ƙai da Kawar da Talauci, Beta Edu.

A wajen zaman akwai kuma wasu daraktoci daga Ma’aikatar Ƙwadago da Samar da Aikin Yi ta Ƙasa.

Gwamnatin TarayyaNLCTUC
Comments (0)
Add Comment