DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnati Ta Kammala Ɗaukar Sabbin Immigration Da Civil Defence, Ta Saki Sunayen Waɗanda Suka Samu

Hukumar Kula da Jami’an Civil Defence, Masu Kula da Gidan Gyaran Hali, Masu Kashe Gobara da kuma Masu Kula da Shige da Fice, CDCFIB, ta saki sunayen waɗanda suka samu nasarar samun aikin Immigration, da Civil Defence.

An bayyana wannan labarin ne a wata sanarwa da aka saki a yau Talata wadda Sakataren Hukumar, Ja’afaru Ahmed ya sanya wa hannu.

Sanarwar ta ce, waɗanda suka samu damar zaunawa rubuta Jarabawar ta Komfuyuta sannan suka je tantancewa da duba takardu ana buƙatar da su ziyarci shafin hukumar a https://cdcfib.career/ domin duba ko sun samu aikin, sannan idan sun samu nasarar ana buƙatarsu da su fitar da slip wanda ke ɗauke da bayanan abubuwan da zasu yi na gaba.

Sanarwar ta ƙara da cewa, aikin shigar da takardu da karɓar takardar ɗaukar aiki ga waɗanda suka samu aikin za a yi su daga ranar Talata, 15 ga watan Agusta zuwa Litinin 4 ga watan Satumba, 2023 a shelkwatar ofishin da ke Abuja.

Sanarwar ta kuma buƙaci kowanne ya je da kansa, inda ta ce ba za a lamunci wani ya je wa wani ba.

Comments (0)
Add Comment