DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Litinin A Matsayin Hutun Bikin Mawlidi

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin, 16 ga Satumba, 2024, a matsayin ranar hutu domin bikin Mawlidi a Najeriya.

Ranar Mawlidi dai rana ce ta tunawa da haihuwar Annabi Muhammad (SAW).

Ministan Harkokin Cikin Gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hutun a madadin gwamnatin tarayya, cikin wata sanarwa da Babbar Sakatariyar ma’aikatar, Dr Magdalene Ajani, ta fitar a yau Juma’a.

Yayin da yake taya al’ummar Musulmi murnar wannan bikin, ministan ya bukace su da su yi amfani da wannan dama wajen yin addu’o’in samun zaman lafiya mai dorewa da kasa mai cike da wadata da adalci.

Ministan ya kuma yi kira ga Musulmi da dukkan ‘yan Najeriya da su rungumi dabi’un hakuri, sadaukarwa, da juriya irin Manzon Allah S.A.W.

Mawlidi
Comments (0)
Add Comment