DA ƊUMI-ƊUMI: Jihar Lagos Ta Rage Kuɗin Hawa Mota Da Kaso 50%

A ƙoƙarinta na rage raɗaɗin janye tallafin man fetur, Gwamnatin Jihar Lagos ta rage kuɗin hawa mota a dukkan motocin haya mallakar jihar da kaso 50 cikin 100, yayinda kuma tai alƙawarin raba kayan abinci ga marassa ƙarfi a jihar.

Da yake magana a gaban ƴan jaridu yau Litinin a Gidan Gwamnatin Jihar Lagos da ke Ikeja, Gwamna Babajide Sanwo-Olu, ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar ta yi wannan yunƙuri ne domin rage raɗaɗin da janye tallafin man fetur ya jawo a kan ƴan jihar.

Gwamnan ya ƙara da cewa, an fitar da tsare-tsaren da motocin hayar da ba na gwamnati ba zasu bi domin rage kuɗin hawa motocinsu da kaso 25 cikin 100.

Gwamna Sanwo-Olu ya ƙara da cewa, ragin kaso 50 cikin 100 na hawa motocin gwamnatin jihar zai fara aiki ne daga ranar Laraba, 2 ga watan Agusta, 2023.

Janye Tallafin MaiJihar LagosTsadar Sufuri
Comments (0)
Add Comment