DA ƊUMI-ƊUMI: Kotu Ta Yi Watsi Da Buƙatar DSS Na Ci Gaba Da Tsare Emefiele

Babbar Kotu da ke Abuja ta yi watsi da buƙatar Hukumar Tsaro da Farin Kaya, DSS, ta ƙarin kwanaki 14 tana tsare da dakataccen Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele.

DSS dai ta gabatar da buƙatarta ga kotun ne a jiya Laraba, inda ta nuna dacewar buƙatar tata saboda sabbin shaidu da ta samu a kan Emefiele.

A hukuncin da ya yanke, Alƙali Muazu ya ce, buƙatar ta DSS, wulaƙanta tsarin tafiyar kotu ne.

Ya kuma ce, kotun tasa ba ta hurumin sauraron ƙarar da aka shigar mata.

Labari Mai Alaƙa: DA ƊUMI-ƊUMI: Kotu Ta Bayar Da Belin Emefiele A Kan Naira Miliyan 20

A watan da ya gabata ne aka gurfanar da Emefiele gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Lagos kan zargin ta’ammuli da makamai ba bisa ƙa’ida ba.

Alƙali Nicholas Oweibo na kotun, ya bayar da belin Emefiele kan kuɗi naira miliyan 20 da kadara mai darajar wannan kuɗin a ranar Talatar da ta gabata tare da umartar Jami’an Kula da Gidan Gyaran Hali su ci gaba da tsare shi kafin ya cika ƙa’idojin belinsa.

To sai dai kuma DSS ta hana jami’an cika umarnin alƙalin, inda suka ƙara kama Emefiele tare da tafiya da shi.

DSSGodwin Emefiele
Comments (0)
Add Comment