DA ƊUMI-ƊUMI: Tinubu Ya Ce Manyan Makarantu Su Dakatar Da Ƙarin Kuɗin Makarantar Da Suka Yi

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci shugabannin makarantun gaba da sikandire na Gwamnatin Tarayya da su guji ƙarin kuɗaɗen makaranta da ake biya da kuma duba yiwuwar gujewa ƙarin a nan gaba don kar iyaye su fuskanci ƙarin shiga cikin matsala.

Ya kuma amince da a samar da motocin bas ga ɗalibai da ke dukkan jami’o’i, makarantun kimiyya da fasaha da kuma makarantun horar da malamai a duk faɗin ƙasar nan.

Mai Bayar da Shawara na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Al’amura na Musamman, Sadarwa da Tsare-tsare, Dele Alake ne ya bayyana hakan a wata sanarwa ta ya sanya wa hannu a yau Litinin.

An yi wa sanarwa take da ‘Gwamnatin Tarayya ta shirya samar da motocin bas ga ɗaliban manyan makarantu, ta kuma cire tsarabe-tsaraben da ke cikin bashin ɗalibai’.

Alake ya ce, an yi hakan ne saboda buƙatar Shugaban Ƙasa ta ganin cewa ɗalibai zasu iya zuwa makarantunsu ba tare da sha wahala ba saboda tsadar sufuri.

Bola Ahmed TinubuDele AlakeKarin Kudin Makaranta
Comments (0)
Add Comment